Fadar shugaban kasa ta umarni dawo da dan jaridar da aka kora daga Villa

Fadar shugaban kasa ta umarni dawo da dan jaridar da aka kora daga Villa

- Fadar shugaban kasa ta umarni dawo da dan jaridar Punch da aka kora daga fadar shugaban kasa a ranar Litini

- Malam Garba Shehu, ya tabbatar da al’amarin a cikin wani sakon jawabi ga shugaban ‘yan jaridar fadar shugaban kasa

- Ya ce shi da mai ba shugaban kasa shawara kan kafofin watsa labarai, Femi Adesina za su warware al’amarin

Fadar shugaban kasa ta ba da umarnin dawo da wakilin jaridar na Punch, Olalekan Adetayo, wanda ke wakilta jaridar Punch a fadar shugaban kasa da ke birnin tarayya Abuja, bayan sa’o’i 10 da aka kore shi daga fadar.

NAIJ.com ta ruwaito cewa, babban kakakin shugaban kasa na musamman, Malam Garba Shehu, ya tabbatar da wannan ci gaba a cikin wani sakon jawabi ga shugaban ‘yan jaridar fadar shugaban kasa, Malam Ubale Musa.

Shehu ya jaddada cewa, sun samu yarda daga shugaban jami’an tsaro na farin kaya,malam Lawal Daura don dawo da Lekan zuwa Villa.

KU KARANTA KUMA: Kotu ya yanke hukunci zama wa tsohon gwamna Neja Babangida Aliyu a kurkuku

Ya ce shi da mai ba shugaban kasa shawara kan kafofin watsa labarai, Femi Adesina za su warware al’amarin.

Zai iya tuna cewa an yi wa Adetayo tambayoyi a ranar Litinin, 24 ga watan Afrilu da rana a ofishin na babban Jami'in tsaro (CSO) ga shugaban kasar a kan wani labarin da dan jaridar ya rubuta game da shugaba buhari kan lafiyarsa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon da wani dan jam'iyyar APC ke bayyana nadamar kasancewa a cikin jam'iyyar saboda masaloli daban-daban da ta ke fuskanta a hannun 'yan jam'iyyar

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel