Abinda ya biyo baya, bayan Osinbajo ya kammala murzan Babachir da tambayoyi

Abinda ya biyo baya, bayan Osinbajo ya kammala murzan Babachir da tambayoyi

- Babachir ya gurfana gaban kwamitin binciken badakalar kudin yankan ciyayi

- Sai da Babachir ya kwashe awanni biyu da rabi yana amsa tambayoyi

Korarren sakataren gwamnatin tarayya Babachir David Lawal ya fita daga ofishin da aka gudanar da bincikensa ba tare da damuwa ko nuna fargaba ba a ranar Talata 25 ga watan Afrilu.

Idan ba’a manta ba shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa kwamitin bincike na mutum uku karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo tare da mashawarcin shugaban kasa a kan harkar tsaro da kuma minista shari’a.

KU KARANTA: An binne gawar Attajiri a kasar Amurka tare da motarsa kamar yadda yayi wasiyya (Hotuna)

Shugaba Buhari ya kafa kwamitin ne don su tabbatar da gaskiyar zargin da ake yi ma Babachir na yin sama da fadi da kudin kula da yan gudun hijira wadanda rikicin Boko Haram ta shafa.

Abinda ya biyo baya, bayan Osinabjo ya kammala murzan Babachir da tambayoyi

Babachir

Jaridar Vanguarda ta ruwaito da misalin karfe daya na rana ne Babachir ya iso fadar shugaban kasa, inda ya zarce kai tsaye zuwa ofishin mataimamin shugaban kasa inda aka gudanar da binciken, sa’annan awanni biyu da rabi kacal ya kwashe yana amsa tambayoyi daga kwamitin.

Majiyar NAIJ.com ta bayyana cewar da misalin karfe 3:25 ne Babachir ya kammala amsa tambayoyin da aka yi masa, bayan fitowarsa an hange shi yana ta shawagi a farfajiyar ofishin shugaban kasar, inda har ma ya dauko wayar salularsa yana kiranye.

Abinda ya biyo baya, bayan Osinabjo ya kammala murzan Babachir da tambayoyi

Osinabjo tare da Babachir

Daga bisani kuma na hange shi tare da mashawarcin shugaban kasa Babagana Munguni daya daga cikin yayan kwamitin dake binciken Babachir suna tattaunawa, yayin da dogaran Babachir ke biye dashi da wasu tarin takardu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yadda tsarin fallasa barayin gwamnati ke aiki

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel