Dattijo mai shekaru 87 a rayuwa ya samu ƙaruwa (Hoto)

Dattijo mai shekaru 87 a rayuwa ya samu ƙaruwa (Hoto)

- Dattijo Baba Garba ya samu haihuwa bayan kwashe shekaru 87

- Matarsa ta farko bata samu haihuwa ba har ta rasu, Amaryar ce ta haihu

Allah majibincin al’amuran duk wanda yayi hakuri da jarabawar da aka yi masa a rayuwa. Wannan shine kwatankwacin yadda za’a iya kwatantan halin da wani dattijo ya samu kansa a ciki.

Dattijo mai suna Baba Garba ya kwashe shekaru 87 ba tare da samun haihuwa ba sai a cikin satin nan Allah ya bashi kyautar ya mace, kamar yadda jaridar Rariya ta ruwaito.

KU KARANTA: An bankaɗo wasu tarin bama bamai da Boko Haram ta binne a Borno

Da fari dai Baba Garba bai samu haihuwa tare da matarsa ta farko ba har Allah yayi mata rasuwa, bayan cikar ajalin matarsa ta farko ne sai Baba Garba ya sake auran wata matashiya.

Dattijo mai shekaru 87 a rayuwa ya samu ƙaruwa (Hoto)

Baba Garba da diyarsa

Sai ga shi cikin ikon Allah amaryar Baba Garb ace keda rabon haifa masa diyarsa ta farko a duniya.

Ko a kwanakin baya sai da NAIJ.com ta kawo muku rahoton wata mata data haifi yan hudu bayan kwashe shekaru 7 bata haihu ba.

Fatan ga Baba Garba shine Allah ya raya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kana da labarin mace mai kamar maza? Kalla

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel