Matasa sun yi ma ɗan majalisar tarayya ruwan duwatsu a Bauchi

Matasa sun yi ma ɗan majalisar tarayya ruwan duwatsu a Bauchi

- Matasa a fusace sun yi ma dan majalisa ruwan duwatsu

- Yan jagaliyan sun yi ma dan majalisar asarar mota da gida

Dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Gamawa dake jihar Bauchi, Garba Mohammed Gololo ya sha da kyar a hannun wasu fusatattun matasa daga mazabarsa a yayin da ya kai ziyara a yankin nasa.

Jaridar Rariya ta rawaito lamarin ya auku ne a ranar Lahadin da ta gabata 23 ga watan Afrilu a yayin ziyarar tasa daya kai a yankin Gololo.

KU KARANTA: Sojoji sun ranta ana kare yayin da yan ƙungiyar asiri suka kashe mutane 20 a Uyo

Matasan sun yi ta jifan dan majalisan har ta kai ga sun farfasa masa mota da lalata masa gidan sa, daga bisani ya ranta ana kare inda ya tsere zuwa garin Gamawa na karamar hukumar Gamawa don kubuta daga matasan yankin nasa.

Matasa sun yi ma ɗan majalisar tarayya ruwan duwatsu a Bauchi

Mohammed Gololo

Sai dai rahotannin da suka ishe majiyar NAIJ.com sun nuna cewa ko a garin Gamawan ma bai tsira daga fushin matasan yankin can ba.

Matasa sun yi ma ɗan majalisar tarayya ruwan duwatsu a Bauchi

Yadda aka lalata gidan Gololo

Idan za a iya tunawa, Honarabul Garba Gololo, yana daga cikin 'yan majalisu guda uku da aka zarge su da yunkurin yin fyade a yayin wata ziyarar aiki da suka kai kasar Amurka a shekarar da ta gabata, wanda hakan ya jawo cece-kuce har ta ga majalisar wakilai ta kafa kwamiti na musamman domin gudanar da bincike kan lamarin.

Matasa sun yi ma ɗan majalisar tarayya ruwan duwatsu a Bauchi

Yadda aka lala gidansa

Wannan ya kara adadin yan majalisun tarayya da suka gamu da fushin al’ummar mazabarsu a Arewa, inda a baya mun kawo muku rahoton wani dan majalisa daga jihar Neja ya sha duka har aka kwantar dashi, said an majalisar yankin Soba na jihar Kaduna, haka shima dan majalisa a Katsina an yayyaga masa riga a Funtua.

Matasa sun yi ma ɗan majalisar tarayya ruwan duwatsu a Bauchi

Kofar gidan Gololo

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Matasa a yi hattara da shan lemun kwalba

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

NAIJ.com
Mailfire view pixel