Babachir ya bayyana a gaban kwamitin bincike na Osinbajo

Babachir ya bayyana a gaban kwamitin bincike na Osinbajo

– Kwamitin Osinbajo ya tasa Babachir a gaba

– Yanzu aka ana can an tarfa Babachir Lawal

– Ana tuhumar Babachir da bada kwangila ba tare da ka’ida ba

A makon jiya ne Shugaba Buhari ya dakatar da Sakataren Gwamnatin sa kuma da shugaban NIA ta tsaro inda ya bada umarni a bincike su. Shugaban kasa ya bada umarni cewa a hukunta duk wanda aka samu da laifi a binciken.

Babachir ya bayyana a gaban kwamitin bincike na Osinbajo

Babachir ya gurfana a gaban kwamitin Osinbajo

Yanzu haka dai labari na zuwa ga NAIJ.com cewa Sakataren Gwamnatin Tarayyar da aka dakatar Babachir David Lawal ya bayyana a gaban kwamitin inda zai sha tambayoyi. Wannan ne dai karo na farko da ya gurfana a gaban kwamitin.

KU KARANTA: An tasa shugaban NIA a gaba jiya

Babachir ya bayyana a gaban kwamitin bincike na Osinbajo

Ana binciken Babachir David Lawal

A makon jiya shugaba Buhari ya nada kwamitin da za tayi wannan bincike cikin makonni biyu. Ana zargin Babachir da bada wasu makudan kwangiloli a yakin Arewa-maso-gabas da rikicin Boko Haram ya afka da su ba tare da ka’ida ba.

A jiya kuna da labari kwamitin da aka nada ta binciki shugaban Hukumar NIA na kasa da aka dakatar. An yi kusan yini guda Ambasada Oye Oke din yana shan tambayoyi. Tun safiya dai Osinbajo da sauran ‘yan kwamitin; Babagana Mungono da Abubakar Malami suka fara aikin.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

An saki Nnamdi Kanu na Biyafara

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel