Yan bindiga sun kashe ƴan sanda 3 da kuma mazauna wata unguwa su 4 a jihar nan

Yan bindiga sun kashe ƴan sanda 3 da kuma mazauna wata unguwa su 4 a jihar nan

- Ƴan sanda uku da kuma mazauna ƙaramar hukumar Water Side su 4 sun rasa rayukansu a hannun wasu da ake zargin ƴan ta’adda ne a jihar Ogun

- Jaridar Punch ta rawaito cewa ƴan sandan sun rasa ransune lokacin da suke ƙoƙarin ceto wani ma’aikaci ɗan ƙasar Sin da ƴan bindigar suka sace

Wani mazaunin yankin ya rasa ransa yayin da ƴan sanda da ƴan ta’adda ke musayar wuta.

Gungun ƴan ta’addar sun kuma kai hari kan gidan wani ɗan kasuwa mai suna Rafi’u Daramola inda sukayi awon gaba da kuɗi kimanin miliyan 4,700,000.

NAIJ.com sun tattro cewa Ƴan ta’addar sun harbe mutane uku mazauna unguwar har lahira kafin su bar unguwar.

Yan bindiga sun kashe ƴan sanda 3 da kuma mazauna wata unguwa su 4 a jihar Ogun

Yan bindiga sun kashe ƴan sanda 3 da kuma mazauna wata unguwa su 4 a jihar Ogun

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari zata samar da ayyukan yi kusan 1,000,000

A cewar wani shugaban al’umma dake yankin:

“Ranar Alhamis ɗin makon da ya gabata wasu ƴan ta’adda sun sace wani ma’aikaci ɗan ƙasar Sin, lokacin da suke tafiya da shi sai ƴan sanda da ke aiki a runduna ta musamman dake yaƙi da fashi da makami suka fara harbe harbe dasu.”

“Yan bindigar sun samu nasarar kashe ƴan sanda 3 da kuma da ɗan asalin yankin mutum ɗaya,” yace.

Rundunar ƴan sanda ta jihar Ogun ta tabbatar da faruwar kisan mutenen ta bakin mai magana da yawunta Abimbola Oyeyemi, an kuma samu nasarar kama mutum daya daga cikin maharan tare da motar hawan da suke amfani da ita.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

An bayar Nnamdi Kanu beli

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel