An zargi dan jarida da ta'addanci, hukuncin da ake yanke masa zai baka tausai

An zargi dan jarida da ta'addanci, hukuncin da ake yanke masa zai baka tausai

- Kotun sojin Kamaru a Yaounde ta zartar da hukuncin daurin shekaru 10 a yau Talata akan Ahmed Abba

- An daure shi ne kan alaka da ayyukan ta’addanci, laifin da babu hujjoji akan dan jaridar da ke aiko wa sashen hausa na RFI da rahotanni daga yankin arewa mai nisa.

- Bayan daurin shekaru 10, kotun kuma ta ci Abba tarar kimanin yuro 85,000

Kotun sojin Kamaru a Yaounde ta zartar da hukuncin daurin shekaru 10 a yau Talata akan Ahmed Abba, kan alaka da ayyukan ta’addanci, laifin da babu hujjoji akan dan jaridar da ke aiko wa sashen hausa na RFI da rahotanni daga yankin arewa mai nisa.

Bayan daurin shekaru 10, kotun kuma ta ci Abba tarar kimanin yuro 85,000.

Amma Lauyan da ke kare shi ya ce za su daukaka kara saboda babu wasu hujjoji da ke tabbatar da Ahmed Abba ya aikata laifin da aka ce an same shi da aikatawa.

An zargi dan jarida da ta'addanci, hukuncin da ake yanke masa zai baka tausai

An zargi dan jarida da ta'addanci, hukuncin da ake yanke masa zai baka tausai

KU KARANTA: Harin kunar bakin wake ya halaka mutane 3 a Maiduguri

NAIJ.com ta samu labarin Shari’ar da ta dauki dogon lokaci ana yi ya janyo hankalin kasashen duniya da kungiyoyin kare Yan Jaridu, musamman Reporters Without Borders.

Abba ya shafe kusan shekaru biyu a tsare cikin yanayi na wahala da azabtarwa tun watan Yulin 2015 da aka kama shi a yankin arewa mai nisa.

Hukumomin RFI sun dade suna allawadai da kama ma'aikacin na sashen hausa ba tare da Kamaru ta gabatar da hujjojin dalilin tsare shi ba.

Kungiyoyin kare hakkin 'Yan Jaridu sun yi watsi da hukuncin inda suka bukaci gaggauta sakin dan Jaridar.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Nan ma iyalan wasu ne da aka kama aka kulle

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel