Allah ya isa! Sama da N7tiriliyan zata iya gyara ta'asar da Boko Haram tayi wa Arewa

Allah ya isa! Sama da N7tiriliyan zata iya gyara ta'asar da Boko Haram tayi wa Arewa

- Gwamnatin tarayyar Najeriya za ta kashe sama da naira tiriliyon biyar wajen sake gina arewa maso gabas da ‘yan ta’adda ta Boko Haram ta lalata

- Shugaban karamin kwamitin shirin shugaban Najeriya na sake gina yankin arewa maso gabas Hon. Yusuf Captain Buba mai wakiltar mazabar Hong da Gombi ya ba da bayanin haka

Shugaban karamin kwamitin shirin shugaban Najeriya na sake gina yankin arewa maso gabas Hon. Yusuf Captain Buba mai wakiltar mazabar Hong da Gombi ya ba da bayanin haka a wata hira da ya yi da majiyar mu a Yola fadar jihar Adamawa lokacin da ya ke amsa tambayar dalilan da suka sa shirin ke tafiyar hawainiya wanda ya danganta da rashin sanya hanu kan kasafin kudin bana.

Shirin sake gina arewa maso gabas inji Hon Yusuf Captain Buba zai hada da gina asibitoci, makarantu, wuraren ibada, samar da muhimman kayan jin dadin rayuwa,tsaro, wutar lantarki, samarwa mata da matasa jari da kuma tallafi ga ‘yan kasuwa da suka yi asarar hajojin su.

NAIJ.com ta ruwaito cewa matsalar rashin wutar lantarki a yankunan da BokoHaram ya shafa inda suka tarwasa tiransfomomi da lalata wayoyin wuta, gwamnatin tarayya za ta kashe sama da naira biliyan tara inji injiniya Umar Baba Mustapha babban manajan kanfanin samar da wutar lantarki a arewa maso gabas dake da ofishinsa a Yola fadar jihar Adamawa.

Allah ya isa! Sama da N7tiriliyan zata iya gyara ta'asar da Boko Haram tayi wa Arewa

Allah ya isa! Sama da N7tiriliyan zata iya gyara ta'asar da Boko Haram tayi wa Arewa

KU KARANTA: Hukumar NDLEA na neman wata yar Kwaya ruwa a jallo

Ya ce a birnin Maiduguri kadai Boko Haram sun farfasa tiransfomomi sama da saba’in kana kuma suka lalata na’urar da ke baiwa birnin Difa a jumhuryar Nijar wutar lantarki. Daya daga kafar dake samarwa Najerya kudaden musaya da kasashen waje.

Garuruwan da matsalar rashin wutar lantarki ya shafa sakamakon barnar da Boko Haram suka haddasa sun hada da Dambuwa, Bama, Askira Uba, Madagali , Gulak, Gwoza da Michika.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Nan ma dai masu tada kaya baya ne na Biafara

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Tirkashi! Har yanzu akwai al'ummomin da ke riko da al'adan kashe tagwaye a Abuja

Tirkashi! Har yanzu akwai al'ummomin da ke riko da al'adan kashe tagwaye a Abuja

Tirkashi! Har yanzu akwai al'ummomin da ke riko da al'adan kashe tagwaye a Abuja
NAIJ.com
Mailfire view pixel