An kama wata karuwa Aisha Idris bisa sayar da jaririn ta akan N200,000

An kama wata karuwa Aisha Idris bisa sayar da jaririn ta akan N200,000

- Rudunar ‘yan sandan jahar Katsina ta cafke wata matashiya ‘yar shekaru 18 mai suna Aisha Idris a bisa laifin sayar da jarirn ta mai watanni 3 akan Naira dubu dari biyu

- Aisha ‘yar asalin karamar hukumar Rimi ne a jahar Katsina amma ta na zaune a Dakin Tara inda ta ke karuwanci

Kwamishinan ‘yan sandan jahar CP Usman Ali Abdullahi ya bayyana yadda Aisha ta hada baki da wata ma’aikaciyar Asibiti mai suna Ogugua Oko, wacce ta hada ta da matar da ta sayi jaririn.

NAIJ.com ta samu labarin ya ce an kawo rahoton ga ‘yan sanda tun ranar 10 ga watan nan, kuma yanzu haka duk wadanda ke da hannu a cinikayyar na hannun ‘yan sanda.

Ya kara da cewa a binciken da suka yi, sun gano jaririn a kauyen Okuku da ke karamar hukumar Owerri a jahar Imo a hannun wacce ta saye shi mai suna Grace Odoho.

An kama wata karuwa Aisha Idris bisa sayar da jaririn ta akan N200,000

An kama wata karuwa Aisha Idris bisa sayar da jaririn ta akan N200,000

KU KARANTA: Kotu ta bayar da belin Nnamdi Kanu

Rahotan ya bayyana cewa jaririn wanda aka sanya wa suna Victor na cikin koshin lafiya.

Grace Odoho ta fadawa ‘yan sanda cewa ta yi aure na tsahon shekaru 18 ba tare da ta samu ‘ya’ya ba, a don haka ne ta yanke hukuncin sayen jariri.

Ita kuwa Aisha cewa ta yi bata san yadda za ta yi da jaririn ba dama, kuma tana shirin yar da shi ne kafin ta yi tunanin sayar wa.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Nan kuma tambaya akeyi shin ko kuna shan Fanta da Sprite har yanzu?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

NAIJ.com
Mailfire view pixel