Dalilin da yasa na halarci gurfanar Nnamdi Kanu a kotu – Gwamna Ayo Fayose

Dalilin da yasa na halarci gurfanar Nnamdi Kanu a kotu – Gwamna Ayo Fayose

- Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya bada dalilin da yasa ya halarci gurfanar Nnamdi Kanu a yau Talata,25 ga watan Afrilu

- Fayose yayi Magana ga manema labarai a wajen kotu bayan zaman

- Yace Kanu dan Najeriya ne kuma zaluntasa ake ba gaira ba dalili

Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya bada dalilan da yasa ya bayyana a kotu yau Talata, 25 ga watan Afrilu domin shaida gurfanar Nnamdi Kanu.

Fayose wanda ya sanya hulan yan kabilan Igbo ya bayyanawa manema labarai a wajen kotun cewa Nnamdi Kanu dan Najeriya ne kuma ana zaluntasa ne kawai.

Gwamnan yace abin takaici ne ana zaluntan yan Najeriya da dama Kaman yadda akewa Nnamdi Kanu.

Dalilin da yasa na halarci gurfanar Nnamdi Kanu a kotu – Gwamna Ayo Fayose

Dalilin da yasa na halarci gurfanar Nnamdi Kanu a kotu – Gwamna Ayo Fayose

Yace: “Wannan kasanmu ne gaba daya, na zo ganawa da mutanen Igbo ne. ra’ayina shine wani ranan, Kanu zai zamu yanci a wannan kasar tamu mai girma.”

KU KARANTA: An baiwa Nnamdi Kanu beli

Halartan gwamnan ya farantawa mambobin kungiyar IPOB rai. Daga cikin wadanda suka halarci gurfanarwan sune Osita Chidoka da Femi Fani-Kayode.

https://www.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel