Matasan kirista da musulmai ke tsare masallatai da kuma coci a lokacin bukukuwa sallah a Filato

Matasan kirista da musulmai ke tsare masallatai da kuma coci a lokacin bukukuwa sallah a Filato

- Hukumar ‘yan sandan jihar Filato ta kirkiro wata shiri inda matasan addinai biyu ke tsare wajen ibadun ko wane a lokacin murnar sallah

- Hukumar 'yan sandan jihar ta ce ta kirkiro wannan shirin ne domin inganta zaman lafiya da kuma fahimtar tsakanin addinai biyu a jihar

Kwamitin kula da kuma dangantakar na 'yan sanda, (PCRC) a Jihar Filato, ta ce ta kirkiro wata dabarun inda matasan kirista ke tsare masallatai ko kuma idi a duk lokacin da musulmai ke murnar sallah, su kuma matasan musulmai su tsare coci a lokacin da kiristoci ke murnar sallah na su.

Shugaban kwamitin na ‘yan sandan ta shiyar Filato, mista Ola Azeez ya bayyana hakan a lokacin da ya jagoranci kungiyar a wata ziyara ga kwamishinan labarai, Malam Muhammad Nazif a Jos a ranar Litinin, 24 ga watan Afrilu.

Ya ce, hukumar ta kirkiro wannan shirin ne domin inganta zaman lafiya da kuma fahimtar tsakanin addinai biyu a jihar.

KU KARANTA KUMA: Sanata ya bayar da tallafi ga yaron da aka yanke ma hannu a jihar Kebbi (HOTUNA)

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, shugaban tawagar ya neme goyon bayan gwamnatin jihar don tabbatar da nasarar da kungiyar ke kokarin cima.

Nazif ya na cewa ko da yake babu wata albashin da gwamnatin kebiyar kungiyar, amma gwamnatin na bayar da wasu rangwamen kudi wanda zai taimaka wajen gudanar da ayyukan ta.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon tsohon direban Bishof David Abioye wanda ya karbi musulunci yayin da ya yi murabus da cocin Living Faith Church

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel