An kai harin kunar bakin wake Maiduguri

An kai harin kunar bakin wake Maiduguri

-An harin kunar bakin wake wasu kauyuka a jihar Borno

-Rahoto ya nuna cewa mutane 2 sun jikkata bayan wadanda suka mutu

Mutane 3 sun hallaka sanadiyar harin kuna bakin wake da aka kai wurare biyu a Maiduguri, birnin jihar Borno.

A daya daga cikin harin, yarinya yar kunar bakin waken kadai ta hallaka yayinda wasu jami’an tsaro suka tare ta a hanya.

Sauran yan mata 2 da ke tare da ita suka arce a lokacin amma jami’an tsaron suka harbesu kafin su tsira.

A harin na biyu, yar kunar bakin waken ta samu nasarar tayar da Bam din cikin jama’a inda mutane 3 suka hallaka.

An kai harin kunar bakin wake Maiduguri

An kai harin kunar bakin wake Maiduguri

Kakakin hukumar yan sandan jihar Borno, Murtala Ibrahim, a wata sako ga manema labarai yace, “A yau (Litinin) misalin karfe 5 na safe, yan kunar bakin wake 3 sukayi kokarin shigaba kauyen Mamanti a karamar hukumar Jere. Amma jami’an civilian JTf sun taresu.

KU KARANTA: Za'a binciki Jonathan idan an kama shi da laifi - Malami

“A lokacin yarinya yar kunar bakin waken kadai ta hallaka yayinda wasu jami’an tsaro suka tare ta a hanya.

“Sauran yan mata 2 da ke tare da ita suka arce a lokacin amma jami’an tsaron suka harbesu kafin su tsira.”

“Kuma misalin karfe 7 da rabi na safe, an kawar wata harin a Mainari Kanuri, wajen garin maidguri.

“Wani dan Boko Haram wanda ya wayance kamar mai tukin baro ya tayar da Bam da ke cikin baronsa inda ya hallaka tare da wasu mutane 3, yayinda wasu 2 sun jikkata.”

https://www.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC
NAIJ.com
Mailfire view pixel