Yau ce ranar yaki da cutar zazzabin cizon sauro

Yau ce ranar yaki da cutar zazzabin cizon sauro

- Wasu shugabanni a Najeriya sun danganta karuwar cutar zazzabin cizon sauro ga dabi'un jama'a na rashin tsaftace muhallan su

- Hukumar lafiya ta Majalisar Dinikin Duniya ta bayyana cewa a shekara mai zuwa ne za a fara riga-kafin cutar zazzabin cizon sauro

- Wasu na ganin cewa rashin mayar da hankali daga bangaren shugabanni ne ya sa har yanzu aka kasa magance matsalar

Yayin da a yau ake bikin ranar yaki da cutar zazzabin cizon sauro ta duniya, wasu shugabanni a Najeriya sun danganta karuwar matsalar ga dabi'un jama'a na rashin tsaftace muhallan su

Gwamnan jihar Zamfara Alhaji Abdul'Aziz Yari Abubakar, wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, ya ce gwamnatocin kasar ana su bangaren na daukar matakai don magance karuwar zazzabin cizon sauro, sai dai ya ce wajibi ne al'umma sai sun bada gudunmuwar su.

Wasu 'yan Najeriyar dai na ganin rashin mayar da hankali daga bangaren shugabanni shi ne ya sa har yanzu aka kasa magance matsalar zazzabin cizon sauro a kasar.

A cewar hukumar lafiya ta Majalisar Dinikin Duniya, wato WHO, daga shekarar 2001 zuwa yanzu, an samu nasarar hana kamuwa da cutar har sau miliyan 663 a yankin nahiyar Afirka kudu da hamadar Sahara, inda a nan ne ake samun kashi 90 cikin 100 na masu kamuwa da cutar.

Ana dai amfani da hanyoyi daban-daban wajen hana kamuwa da cutar, amma kuma wasu daga cikin hanyoyin da ake amfani da su din na da matukar hadari.

A wani labarin kuma, hukumar lafiya ta duniya, ta ce a karon farko za ta fara riga-kafin cutar zazzabin cizon sauro a kasashe 3 na Afrika da suka hada da Ghana, Kenya da kuma Malawi.

KU KARANTA KUMA: Kamar yadda 300,000 'yan Najeriya na mutuwa a kowane shekara, tsammani abin da za a wa ‘yan Ghana na hana hadarin

NAIJ.com ta ruwaito cewa hukumar ta bayyana cewa a shekara mai zuwa ne za a fara riga-kafin.

Kimanin jarirai 1,800 ne ake sa ran za su amfana da allurar wadda za a kwashe shekaru 2 ana yi.

Kasashen Afrika ne dai suka fi fama da cutar zazzabin cizon sauron, kuma yawancin wadanda ke mutuwa sakamakon kamuwa da ita yara ne.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon farashin kayayyaki a kasuwannin jihar Ogun

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata
NAIJ.com
Mailfire view pixel