Mutuwar sanata Adeleke : Yan sanda sun damke likitan da ya bashi magani

Mutuwar sanata Adeleke : Yan sanda sun damke likitan da ya bashi magani

- Jami’an tsaro sun sun damke liktan da ya baiwa marigayi Adeleke magani lokacin da yayi kukan ciwon kafa

- Sanata Adeleke wanda ke cikin koshin lafiya ranan Asabar,22 ga watan Afrilu kuma ya halarci wani taro

- Marigayin wanda yayi gwamnan jihar Osun na farko, ya rasu ranan Lahadi

Daya daga cikin ma’aikatan marigayi Adeleke yace likitan da kula da sanatan , Dakta Ade, na hannun hukuma domin gudanar da bincike.

Jaridar Punch ta bada rahoton cewa majiya tace an damke likitan ne da safiyar Litinin, 24 ga watan Afrilu, bisa ga sakamakon binciken asibiti cewa Adeleke ya rasu ne sanadiyar bashi magani fiye da abinda ya kamata lokacin da yace kafarsa na masa ciwo.

NAIJ.com ta tattaro cewa duk da cewa sakamako asibitin bai bayyana ga jama’a ba, wani ma’aikacin marigayin yace an damke likitan ranan Litinin, 24 ga watan Afrilu.

Mutuwar sanata Adeleke : Yan sanda sun damke likitan da ya bashi magani

Mutuwar sanata Adeleke

Anyi kokarin tabbatar da wannan labara daga bakin kwamishanan yan sandan jihar Osun, Mr Fimihan Adeoye, ta wayan tarho amma bai daga wayan ba.

KU KARANTA: Goodluck yayi babban furuci akan Attahiru Jega

An samu jita-jitan cewa wasu makiyansa sun bashi guba ne saboda lafiyanshi kalau ranan asabar, 22 ga watan Afrilu a wata taron da ya halarta kuma ya tarbi baki har karfe 2 na dare kafin ya kwanta.

https://www.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel