Jega ya bani kunya – Goodluck Jonathan

Jega ya bani kunya – Goodluck Jonathan

- Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan yace tsohon shugaban hukumar INEC, Attahiru Jega, ya bashi kunya

- Tsohon shugaban kasan ya fadi a wani takardan da Segun Adeniyi, ya rubuta inda yace bai ji dadin yadda Jega ya gudanar da zaben 2015 ba

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan yace yaji kunyan yadda tsohon shugaban hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta INEC, Attahiru Jega, ya gudanar da zaben shugaban kasan 2015.

NAIJ.com ta tattaro cewa tsohon shugaban kasa ya bayyana hakan ne a wata littafin da Segun Adeniyi, ya rubuta mai suna ‘Against the Run of Play’, cewa bai ji dadin yadda Jega ya gudanar da zaben 2015 ba.

Jonathan yace : “ Jega ya bani kunya saboda har yanzu ban fahimci dalilin da yasa yake halayen da yayi makonni kafin zabe ba.”

Jega ya bani kunya – Goodluck Jonathan

Jega ya bani kunya – Goodluck Jonathan

“A makon farko ba watan Febrairun 2015 lokacin da kashin 40 cikin 100 na mutane kawai suka karbi katin zaben su, Jega yace INEC ta shirya gudanar da zaben duk da cewa miliyoyin mutane ba zasu damu daman zabe ba.”

Amurkawa na zugashi yayi abinda ya ga dama duk da cewa ba zasu yarda irin hakan ya faru a kasarsu ba. Shin ta yaya zamu zamu hana kusan kasha ukun mutane zabe kuma kuce zaben gaskiya be.

“Abin mamakin shine ko yan adawa sun goyi bayana akan rashin gudanar da zaben da zai karashe cikin rudani.

“Lokacin da jami’an tsaro suka bukaci Karin lokaci domin dakile rashin tsaro, dalilan masu gamsarwa na.

“An wata Febrairun 2015, zai yi wuya a gudanar da zabe a Gombe, Adamawa, Borno da Yobe. Amma lokacin da makaman d ake bukata suka karaso , soji sun yi amfani da su wajen dakile yan Boko Haram din da ke kokarin tayar da tarzoma lokacin zabe.”

https://www.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel