Hukumar NDLEA ta bayar da mayar farautar wata mai safaran miyagun kwayoyi (HOTUNA)

Hukumar NDLEA ta bayar da mayar farautar wata mai safaran miyagun kwayoyi (HOTUNA)

- Hukumar dake kula da masu fataucin mugayen kwayoyi (NDLEA) ta bayar da mayar farauutar wata da ake zargin mai safarar miyagun kwayoyi ce a jihar Lagas

- Ana neman matar ne ruwa a jallo kan zargin safaran hodar iblis mai nauyin 1.595kg a watan Fabrairu na 2017

An kafa mayar farautar wata mai safarar miyagun kwayoyi kuma sananiya a Lagas, Fumilola Arike Ogbuaya,wacce ke da hannu cikin safarar hodar iblis mai nauyin 1.595kg daga Lagas zuwa kasar Saudiyya.

A cewar kakakin hukumar NDLEA, Mitchell Ofoyeju, hukumar na binciken kadarorin matar na biliyoyin naira.

NAIJ.com ta tattaro cewa hukumar ta fara gudanar da bincike a kan wacce ake zargin bayan kama wata mai safarar miyagun kwayoyi mai suna, Odeyemi Omolara Morayo, wacce aka fi sani da Ariyo Monsurat Olabisi.

Hukumar NDLEA ta bayar da mayar farautar wata mai safaran miyagun kwayoyi (HOTUNA)

Hukumar NDLEA ta bayar da mayar farautar wata mai safaran miyagun kwayoyi

Binciken da hukumar keyi cikin al’amarin Morayo ne ya jaza ma Ogbuaya wacce aka gayyata a lokacin don amsa tambayoyi.

KU KARANTA KUMA: Hukumar NSCDC ta tura hafsohi 95 domin tabbatar da tsaro a kotuHukumar NSCDC ta tura hafsohi 95 domin tabbatar da tsaro a kotu

Jami’an hukumar sun kai farmaki gidan Ogbuaya bayan ta ki amsa gayyata amma aka neme ta aka rasa ko sama ko kasa.

Bayan wani bincike cikin al’amarin Ogbuaya hukumar ta gano cewa mai laifin nada kadarori da dama da ya kai kimanin biliyoyin naira.

An gano cewa matar da ta fito daga jihar Osun nada kadarori a jihohin Lagas, Ogun da Osun.

Muhammad Mustapha Abdallah, shugaban hukumar ta NDLEA ya sha alwashin gano duk wasu masu safarar miyagun kwayoyi a kasar.

Ya bukaci al’umma da su ba hukumar hadin kai idan suka samu bayanin inda Ogbuaya ta ke.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shin har yanzu kana shan wadannan lemukan na kwalba?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Tirkashi! Har yanzu akwai al'ummomin da ke riko da al'adan kashe tagwaye a Abuja

Tirkashi! Har yanzu akwai al'ummomin da ke riko da al'adan kashe tagwaye a Abuja

Tirkashi! Har yanzu akwai al'ummomin da ke riko da al'adan kashe tagwaye a Abuja
NAIJ.com
Mailfire view pixel