Zazzabin cizon sauro: Kamar yadda 300,000 'yan Najeriya na mutuwa a kowane shekara, tsammani abin da za a wa ‘yan Ghana na hana hadarin

Zazzabin cizon sauro: Kamar yadda 300,000 'yan Najeriya na mutuwa a kowane shekara, tsammani abin da za a wa ‘yan Ghana na hana hadarin

- Hukumar ta bayyana cewa a shekara mai zuwa ne za a fara riga-kafin

- Hukumar lafiya ta duniya ta ce gwajin za iya magance matsalar cutar da kashi 40 cikin 100

- Hukumar ta zabi Ghana da Kenya da Malawi ne saboda amfani da gidajen sauro

- Kasashen Afrika suka fi fama da cutar zazzabin , kuma yawancin wadanda ke mutuwa yara ne

Hukumar lafiya ta duniya ta ce a karon farko za ta fara riga-kafin cutar zazzabin cizon sauro a kasashe uku na Afirka da suka hada da Ghana da Kenya da kuma Malawi.

Hukumar ta bayyana cewa a shekara mai zuwa ne za a fara riga-kafin.

NAIJ.com ya tara cewa, kimanin jarirai 1,700 ne ake sa ran za su amfana da allurar wanda za a debi shekaru biyu ana yi.

KU KARANTA: Yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya

Shellar da hukumar ta yi ta biyo bayan wani gwaji na matakin farko da aka yi, wanda ya nuna cewa allurar ta hana mutane 4 daga cikin 10 kamuwa da zazzabin cizon tsauro.

Hukumar lafiya ta duniya ta ce gwajin za iya magance matsalar cutar da kashi 40 cikin 100.

Kasashen Afirka ne suka fi fama da cutar zazzabin, kuma yawancin wadanda ke mutuwa yara ne

Kasashen Afirka ne suka fi fama da cutar zazzabin, kuma yawancin wadanda ke mutuwa yara ne

Cutar cizon sauro dai tana hallaka mutane a kalla 500,000 a duk shekara.

Hukumar ta zabi Ghana da Kenya da Malawi ne saboda suna gudanar da manyan shirye-shirye na magance cutar da amfani da gidajen sauro duk da cewa kasashen na fama da cutar zazzabin cizon sauron.

KU KARANTA: Dole Buhari ya zo neman waraka daga gare ni tun kafin lokaci ya kure – Satguru Maharaji

Sai dai duk da nasarar da wadannan kasashe suka samu akwai wadanda ke kamuwa da cutar miliyan 212 wanda ke janyo mutuwar 429,000 mutane.

Kasashen Afrika ne suka fi fama da cutar zazzabin , kuma yawancin wadanda ke mutuwa yara ne.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wannan NAIJ.com bidiyo ya nuna 'yan Najeriya sun yi magana bisa da kudi N1500 na kiwon lafiya ma kowa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Buhari ya taya Iran da Iraqi bakin cikin girgizan kasa da ya afku kwanan nan

Buhari ya taya Iran da Iraqi bakin cikin girgizan kasa da ya afku kwanan nan

Buhari ya taya Iran da Iraqi bakin cikin girgizan kasa da ya afku kwanan nan
NAIJ.com
Mailfire view pixel