Yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya

Yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya

- Kwamitin bincike da shugaba Muhammadu Buhari ya kafa domin binciken sakataren gwamnatin kasar Babachir David Lawal, da shugaban hukumar leken asirin kasar ta fara gudanar da aikinsa

- Masana ‘yan najeriya na ganin akwai bukatar a fadada binciken ci hanci da rashawa zuwa fadar shugaban kasar

Yayin da kwamitin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kafa domin binciken sakataren gwamnatin kasar Babachur David Lawal, da shugaban hukumar leken asirin kasar, NIA, ke fara gudanar da aikinsa, masana na ganin akwai bukatar a fadada binciken zuwa fadar shugaban kasar.

Kamar yadda aka sani, yaki da cin hanci da rashawa na cikin batutuwan da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sha alwashin aiwatarwa tun lokacin da yake yakin neman zabe. Kuma 'yan Najeriya da dama na ganin babu mutumin da ya cancanci ya aiwatar da wannan shiri kamar sa musamman idan aka yi la'akari da dattakunsa da kuma tarihinsa na kyamar cin hanci.

NAIJ.com ta ruwaito cewa, a baya bayan nan ne shugaba Buhari ya dakatar da sakataren gwamnatin sa Mista Babachur David Lawal da kuma shugaban hukumar leken asirin kasar, NIA, bisa zargin laifukan cin hanci da rashawa, wanda kuma nan take shugaba Buhari ya nada mataimakinsa Osinbajo da ya jagoranci gudanar da bincike game da laifin da ke kan Babachir Lawal da shugaban hukumar ta NIA.

KU KARANTA KUMA: Kuma, kotun CCT tace fara gurfanar da Saraki da Jastis Ngwuta kulli yaumin

To sai dai kuma, yayin da ake fara wannan bincike har yanzu ‘yan Najeriya na ganin akwai wasu jami’an gwamnatinsa da dama da ake zargin da cin hanci, cikinsu har da, wanda ake zargi da mallakar manyan gidaje na sama da dala miliyan 1.5 a birnin Dubai da ke Hadaddiyar Daular Larabawa. Haka nan kuma, ga batun badakalar MTN, lamarin da yanzu haka yan kasar ke tsokaci.

Masu sharhi na ganin lokaci ya yi da shugaba Buhari zai dauki matakin ba sani ba sabo, a yakin da yake yi da cin hanci da rashawa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kali yadda sariki Sanusi ya caccaki shugabanin najeriya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel