Dole Buhari ya zo neman waraka daga gare ni tun kafin lokaci ya kure – Satguru Maharaji

Dole Buhari ya zo neman waraka daga gare ni tun kafin lokaci ya kure – Satguru Maharaji

- Shugaban One Love Family, Satguru Maharaji ya shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari da yayi gaggawan zuwa neman waraka ga rashin lafiyarsa daga gare shi

- Ya ce dole Buhari ya zo neman waraka daga gare shi tun kafin lokaci ya kure

Shugaban One Love Family, Satguru Maharaji ya shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari da yayi gaggawan zuwa neman waraka ga rashin lafiyarsa daga gare shi.

NAIJ.com ta samu labarin cewa Maharaji ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 24 ga watan Afrilu lokacin da yake jawabi gay an jarida bayan wani taro na tsawon mako daya wanda yayi murnar cikar sa shekaru 30 da kafa kauyen Maharaji, a hanyar babban titin Lagas-Ibadan a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

“Ya kamata ya je neman taimako daga bakin mutun ba wai fararen fata a Landan ba.

Dole Buhari ya zo neman waraka daga gare ni tun kafin lokaci ya kure – Satguru Maharaji

Satguru Maharaji ya ce dole Buhari ya zo neman waraka daga gare shi tun kafin lokaci ya kure

“Ku tuna lokacin karshe da zai fita daga kasar domin ganin likita, Ni kadai ne nace zai dawo lafiya. Abun da nake nufi a nan shine ya kamata muyi amfani da ikonmu a nan mu taimaki kawunan mu.

KU KARANTA KUMA: Abu mai karya zuciya: kalli jarumin soja da yan Boko Haram suka kashe

“Bazai yiwu ka zauna kana cewa Maharaji ji ba musulmi bane ko kuma ba Kirista bane. Shin Allah Musulmi ne? don haka, idan zai iya zuwa gare ni, zan warkar da shi”, inji shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fitar da kasar daga koma bayan tattalin arziki?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel