Yan Najeriya 300,000 ne ke hallaka sanadiyar zazzabin cizon saura – Kasar Amurka

Yan Najeriya 300,000 ne ke hallaka sanadiyar zazzabin cizon saura – Kasar Amurka

-Kasar Amurka ta bada tallafin $495 million domin yaki da cutan zazzabin sauro

-Tace akalla yan Najeriya miliyan 80 ne ke kamuwa da cutan kowani shekara

A yunkurin murnan zagayowar ranan zazzabin cizon sauro, kasar Amurka tace akalla mutane 300,000 ne ke mutuwa sanadiyar zazzabi cizon sauro a Najeriya.

An bayyana wannan yayinda aka bayar da agajin $495 million domin yaki da zazzabin cizon sauro a jihohi 11 cikin shekaru 6.

A jawabin da manema labarai suka samu jiya a Abuja, daga hannun ofishin jakadancin kasar Amurka, mataimakin jakadan., Dabid Young, ya bayyana cewa akalla yan Najeriya miliyan 80 ne suke kamuwa da ciwon zazzabin cizon sauro kowani shekara.

Yan Najeriya 300,000 ne ke hallaka sanadiyar zazzabin cizon saura – Kasar Amurka

Yan Najeriya 300,000 ne ke hallaka sanadiyar zazzabin cizon saura – Kasar Amurka

Game da cewarsa, shirin shekaran nan mai take ‘ Menene ruwan da zaka taka’ na son kawar da ciwon zazzabin cizon sauron ne gaba daya.

“A kowani shekarar, akalla mutane miliyan 80 ne ke kamuwa kuma mutane 300,000 suna hallaka. Kasar Amurka ta hanyar shirin shugaban kasa akan zazzabin sauro da hukumar agajin waje na kasar Amurka tana shirye da taimakawa wajen sanar da mutane yadda zasu kare kansu da kula da cutan.

KU kARANTA : Ruwa mai karfi yayi gyar a jihar Nasarawa

“Gwajin kwarai da wuri nada muhimmanci akan dakile cutan. Gwajin cutan cizon sauro nada muhimmanci saboda rashin gwajin kwarai kan jawo cigaban cutan wanda zai iya hallaka rayuka.”

“A shekarar 2015, Najeriya ta zabi shirin gwaji, kula da bibiya domin dakile cutan zazzabin cizon sauri. Kawar da cutan zai taimaka wajen rashin fashin zuwa makarantan yara, bunkasa aikin ma’aikata da kuma rage kudin asibiti.

“Shi yasa kawar da cutan zazzabin sauro bai gushe babban abinda kasar Amukr ke baa tallafi akai ba. “

https://www.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel