Babu jami’an da suka ajiye aikinsu – Fadar shugaban kasa

Babu jami’an da suka ajiye aikinsu – Fadar shugaban kasa

- Fadar shugaban kasa ta musanta batun jita-jitar dake yaduwa na cewa shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa sun ajiye aiki

- Malam Garba Shehu, Babban mashawarcin shugaban kasa kan harkokin yada labarai, ya musanta batun yayin tattaunawarsa da manema labarai jiya a Abuja

Fadar shugaban kasa ta musanta batun jita-jitar dake yaduwa na cewa shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari, da Darakta Janar na hukumar tsaron farin kaya (DSS), Lawal Daura, sun ajiye aikin su.

Malam Garba Shehu, Babban mashawarcin shugaban kasa kan harkokin yada labarai, ya musanta batun yayin tattaunawarsa da manema labarai jiya a Abuja.

KU KARANTA KUMA: Ruwan sama mai iska ya tafi da gidaje a jihar NasarawaRuwan sama mai iska ya tafi da gidaje a jihar Nasarawa

Ya kuma alakanta jita-jitar wadda ta rika zagaya dandalin sada zumunta na kasar nan da cewa wata hanya ce ta neman bata sunan jami’an.

Babu jami’an da suka ajiye aikinsu – Fadar shugaban kasa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Malam Garba Shehu ya kara da cewa, yayinda jita-jitar ke yada dandalin sada zumunta su kuwa manyan jami’an biyu na can na ci gaba da gudanar da aikin da aka dora musu nauyi, yana mai cewa yanzu haka Abba Kyari na can kasar China don gudanar da wani aiki.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Har gobe shugaban kasa Muhammadu Buhari na da farin jinin jama'a.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel