EFCC za ta maka wani tsohon Gwamna a Kotu

EFCC za ta maka wani tsohon Gwamna a Kotu

– A yau ake tunani Hukumar EFCC za ta shiga Kotu da tsohon Gwamnan Neja

– Tun jiya muka samu labari cewa Ranar Talata za a gurfanar da Babangida Aliyu

– Jama’a na shirin kunyata Gwamnan idan an fito da shi

NAIJ.com na samun labari cewa a yau Talata ne ake shirin gurfanar da tsohon Gwamnan Jihar Neja watau Muazu Babangida Aliyu a Garin Minna babban Birnin Jihar na Neja a babban Kotun tarayya.

Ana dai zargin Muazu Babangida Aliyu da wasu tarin laifuffuka a lokacin da ya rike kujerar Gwamnan Jihar na shekaru 8 daga 2007 har zuwa 2015. Tun kwanaki dama dai Hukumar EFCC ta damke sa bayan an bayyana cewa bai amsa gayyata ba.

KU KARANTA: Gwamna El-Rufai yayi magana game da Zakzaky

EFCC za ta maka wani tsohon Gwamna a Kotu

Hukumar EFCC za ta maka tsohon Gwamnan Neja a Kotu

Labarin da mu ke ji dai shi ne Jama’an gari na shirin tarbar tsohon Gwamnan na su da jifa yayin da aka shirya shigar da shi kotu. Dalilin haka ne aka tanadi Jami’an tsaro domin hana kawo wani rikici.

Kuna da labari jiya an dauki dogon lokaci har kusan yini guda shugaban NIA din da aka dakatar na kasa yana shan tambayoyi. Tun safiya dai Osinbajo da sauran ‘yan kwamitin da aka nada suka fara aikin.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ana kokarin gano barayin Gwamnati

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Buhari ya taya Iran da Iraqi bakin cikin girgizan kasa da ya afku kwanan nan

Buhari ya taya Iran da Iraqi bakin cikin girgizan kasa da ya afku kwanan nan

Buhari ya taya Iran da Iraqi bakin cikin girgizan kasa da ya afku kwanan nan
NAIJ.com
Mailfire view pixel