Yanzu talaka zai ji dadi-Gwamnatin Tarayya

Yanzu talaka zai ji dadi-Gwamnatin Tarayya

– Ministar tattalin arziki ta bayyana cewa yanzu abu guda ke gaban ta

– Kemi Adesoun tace yanzu kuma ta talaka ta ke

– Talakawa da dama dai na kuka da wannan Gwamnati

NAIJ.com na samun rahoto cewa Ministar kudi ta kasa watau Kemi Adeosun ta bayyana cewa yanzu abin da ke gaban ta shi ne talakan Najeriya ya samu ya amfana. Ministar tace yanzu ta talakawan Najeriya ta ke.

Yanzu talaka zai ji dadi-Gwamnatin Tarayya

Yanzu ta talaka mu ke-Adesoun

Ministar ta dauki kusan shekara guda tana shiryawa inda har aka zana mafita daga kangin tattalin arzikin da Najeriya ta burma ciki. Ministar ta bayyana wannan ne a wata ganawa da tayi da Jami’an bankin Duniya da IMF mai bada lamuni.

KU KARANTA: Naira ta kara yin kasa a kasuwa

Yanzu talaka zai ji dadi-Gwamnatin Tarayya

Ana ma Shugaba Buhari lakabi da 'Mai talakawa'

Daga cikin matsalolin da ake fama da su a Najeriya akwai rashin isassun gidajen zama don haka ne wannan Gwamnati ke shirin gina gidaje. Ministar tace za kuma ayi kokari wajen ganin an wadata Najeriya da abinci da tsaro da ma lantarki.

Akwai kishin-kishin din Shugaba Buhari na neman sabon Sakataren Gwamnatin Tarayya kuma daga cikin wadanda ake tunani zai maye gurbin akwai Hameed Ali na Hukumar kwastam wanda ya saba aiki da shugaba Buhari tun ba yau ba.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Jama'a na bayan Shugaban kasa Buhari

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata
NAIJ.com
Mailfire view pixel