Tir: Naira ta sha kasa a kasuwa

Tir: Naira ta sha kasa a kasuwa

– Farashin Naira na yayi kasa kwarai a kasuwa

– Dalar Amurka ta tashi a halin yanzu

– CBN na kokarin cigaba da tsagaita tashin dala

NAIJ.com na samun labari cewa Naira na shan kashi a kasuwar canji daga jiya bayan da ta rage daraja. Wannan na zuwa ne bayan yunkurin da babban bankin CBN tayi na saida Dalolin ga sauran masu bukata.

Tir: Naira ta sha kasa a kasuwa

Gwamnan CBN Emefiele

Muna samun rahoto cewa Dala ta koma N390 a hannun ‘yan kasuwa a farkon wannan makon. Idan ba a manta a kasuwar kudin kasar waje dai an saida Dala ne a kan N315 zuwa N316. Kamar dai yadda mu kace a hannun ‘yan kasuwar Dalar tana kan N385.

KU KARANTA: Mai kudin Duniya ya bayyana abin mamaki

Tir: Naira ta sha kasa a kasuwa

Abu ya lalace: Naira ta sha kasa

Haka kuma Naira ta kara fadi a kan Dalar Fan Sterling ta Ingila da N5 haka nan ta sha kasa a hannun Dalar EURO ta Turai. Wancan makon farashin EURO yana kan N410 yayin da Fan Sterling na kasar Ingila yake N495.

Babban bankin kasar na CBN na cigaba da kokarin ganin maganin tashin dalar inda aka kawo sababbin tsare-tsare na sakin dalar ga ‘yan canji da sauran masu bukata kai-tsaye

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Farashin kaya a kasuwannin kasar Yarbawa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel