Ba ka san na gida ba: An fara binciken su Babachir David Lawal

Ba ka san na gida ba: An fara binciken su Babachir David Lawal

– Kwamitin da shugaba Buhari ya nada ya binciki su Babachir ta soma aiki

– Shugaba Buhari ya dakatar da Sakataren Gwamnatin da shugaban NIA

– Shugaban kasa ya bada umarni cewa a hukunta duk wanda aka samu da laifi

NAIJ.com na samun labari cewa a jiya ne kwamitin nan da shugaba Buhari ya nada ta binciki Sakataren Gwamnati da shugaban Hukumar NIA na kasa ta zauna inda ta gayyaci shugaban Hukumar NIA din da aka dakatar.

Ba ka san na gida ba: An fara binciken su Babachir David Lawal

Shugaban NIA da Shugaba Buhari ya dakatar

Majiyar mu ta bayyana cewa an dauki dogon lokaci har kusan yini guda shugaban NIA din da aka dakatar yana shan tambayoyi. Tun safiya dai Osinbajo da sauran ‘yan kwamitin Babagana NSA Mungono da kuma Ministan shari’a Abubakar Malami suka fara aikin.

KU KARANTA: An fara harin kujerar Babachir

Kuna da labari cewa ana tuhumar Ambasada Oye Oke da kin bayani game da wasu makudan kudi kusan Naira Biliyan 15 da hukumar sa ta ajiye tun lokacin shugaba Jonathan da sunan wani aiki da za a yi.

Dama tun can Kwamitin ta tattara sunayen wadanda ake bukatar a gurfanar domin samun karin bayani. Shi kuwa shugaban kasar yace duk wanda aka samu da laifi a dakatar da shi ba tare da wata-wata tun kafin a kammala binciken.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ana tona asirin barayi a Najeriya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel