Fadar shugaban kasa ta yi bayani kan fitar da wani dan rahoto daga Aso Villa

Fadar shugaban kasa ta yi bayani kan fitar da wani dan rahoto daga Aso Villa

- Fadar shugaban kasa ta nisanci kanta daga fitar da wani wakilin jaridar Punch a fadar shugaban kasa

- Wakilin, Olalekan Adetayo ya yi wani rubutu game da kiwon lafiyar shugaban kasa Buhari wanda ta yi sanadiyar babban jami'in tsaron shugaban kasa fitar da shi a ranar Litinin da yamma

Fadar shugaban kasa ta mayar da martani ga rahoton cewa Olalekan Adetayo, wakilin jaridar Punch wanda aka fitar daga fadar shugaban kasa.

Babban jami'in tsaron shugaba Buhari, Bashir Abubakar Bindawa ya kore Adetayo daga fadar shugaban kasa a ranar Litinin da rana, 24 ga watan Afrilu, a kan wani labarin a kan lafiyar shugaban kasa.

NAIJ.com ta ruwaito cewa a wasu jerin bayanai a shafin twitter na kakakin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Femi Adesina ya ce, ba a shawarci fadar shugaban kasa ba kafin wannan mataki da aka dauka. Ya ce shugaba Buhari na jajirce wajen 'yanci ‘yan jaridu kuma ya ce za a sasanta al'amarin.

Fadar shugaban kasa ta yi bayani kan fitar da wani dan rahoto daga Aso Villa

Babban jami'in tsaron shugaban kasa da wakilin jaridar Punch da aka kora a fadar shugaban kasa

KU KARANTA KUMA: An fara harin kujerar Sakataren Gwamnati; Ka ji wanda ake sa rai?

Jaridar ta rahoto a ranar Lahadi, 23 ga watan Afrilu cewa akwai sabuwar tashin hankali a fadar shugaban kasa a kan kiwon lafiyar shugaba Buhari.

A halin yanzu, 'yan Najeriya da dama sun yi Allah wadai da matakin da shi CSO ya dauka kan rahoton.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon inda wani matashi ke tambayar 'yan Najeriya cewa, in Buhari bai da lafiya, su ma ba su da lafiya ne.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel