An fara harin kujerar Sakataren Gwamnati; Ka ji wanda ake sa rai?

An fara harin kujerar Sakataren Gwamnati; Ka ji wanda ake sa rai?

– Shugaba Buhari ya dakatar da Sakataren Gwamnatin Tarayya

– Shugaban kasa ya bada umarni a bincike sa a kuma hukunta mai laifi

– Jama’a da dama sun fara harin wannan kujerar

An fara harin kujerar Sakataren Gwamnati; Ka ji wanda ake sa rai?

Watakila a nada Hamid Ali a matsayin sabon SGF

NAIJ.com ta kawo maku labari cewa akwai kishin-kishin din Shugaba Buhari na neman sabon Sakataren Gwamnati bayan da zargin da ke kan Mr. Babachir Lawal su ka yi girma inda har aka dakatar da shi.

Wata Majiyar kamar yadda mu ke ji na tabbatar da cewa Babachir Lawal din ba zai dawo kujerar sa ba. Yanzu dai an fara neman wanda zai maye gurbin. Daga cikin wadanda ake tunani kuma akwai Hameed Ali na Hukumar kwastam wanda ya saba aiki da shugaba Buhari tun ba yau ba.

KU KARANTA: An yabawa Shugaban kasa Buhari

An fara harin kujerar Sakataren Gwamnati; Ka ji wanda ake sa rai?

Ba mamaki cikin Ministocin Buhari za a nemo SGF

Haka kuma ana tunani watakila a dauki Ministan Ilmi Adamu Adamu ya maye kujerar wanda shi ma na-kusa da Buhari ne, tun da can har ya masa Sakatare a PTF. Tuni ma dai an fara binciken su Babachir Lawal din.

Har wa yau a cikin masu neman kujerar akwai irin su Ikeobasi Mokelu da Dr. Fatima Balla Abubakar kamar yadda mu ke samun labari. Kuma dai wasu na goyon bayan Tony Momoh da Ministan Kimiyya Ogbonnoya Onu.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ya kamata Gwamnati ta sasanta da masu neman Biyafara

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

NAIJ.com
Mailfire view pixel