Dakarun sojin Najeriya sun gano boyayyun makamai a kudancin Kaduna

Dakarun sojin Najeriya sun gano boyayyun makamai a kudancin Kaduna

- Rundunar sojin Najeriya sun gano boyayyun makamai a kudancin Kaduna

- Kakakin rundunar sojin Najeriya Janar Sani Usman ne ya sanar wa manema labarai

- An gano makaman da aka boye a kauyukan, Gwaska, Dangoma, Angwan Far da Bakin Kogi dake yankin kudancin Kaduna

Kakakin rundunar sojin Najeriya Janar Sani Usman ya sanar wa manema labarai cewa dakarun sojin Najeriya sun gano wasu makamai masu yawa da aka boye a kauyukan, Gwaska, Dangoma, Angwan Far da Bakin Kogi dake yankin kudancin Kaduna din.

Sojin ta samu nasaran hakan ne a ci gaba da aikin da ta ke yi a dazukan kudancin Kaduna mai suna ‘Operation Harbin Kunama’.

Makaman da aka gano sun hada da bindigogi dirar hannu, da alburusai da dai sauransu.

Dakarun sojin Najeriya sun gano boyayyun makamai a kudancin Kaduna

Dakarun sojin Najeriya sun gano boyayyun makamai a kudancin Kaduna

Wannan shiri na ‘Operation Harbin Kunama’ ya hada da dazukan da sukayi iyaka da jihohin Bauchi, Kano da jihar Filato.

KU KARANTA KUMA: Sojoji sun ranta ana kare yayin da yan ƙungiyar asiri suka kashe mutane 20 a Uyo

A wani al'amari makamancin wannan, NAIJ.com ta rahoto cewa akalla mutane 20 ne suka rigamu gidan gaskiya a garin Oku Iboku na jihar Akwa Ibom yayin da wasu shu’uma matasa suka kai hari.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wani soja mai ritaya ya yi kira ga gwamnati da ta sasanta da kungiyar IPOB.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

NAIJ.com
Mailfire view pixel