Hukumar NSCDC ta tura hafsohi 95 domin tabbatar da tsaro a kotu

Hukumar NSCDC ta tura hafsohi 95 domin tabbatar da tsaro a kotu

-An gurfanar a tsohon gwamnan jihar Neja, Babangida Aliyu, a babban kotun jiha

-Ana tuhumarsa da laifin almundahanan makudan kudi lokacin da yake ofis

Hukumar yan sandan farin kaya wato NSCDC a ranan Litinin ta tura jami’anta 95 domin tabbatar da tsaro a babban kotun garin Minna yayinda hukumar hana almundahana da yiwa tattalinn arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Neja, Babangida Aliyu.

Babangida Aliyu wanda yayi gwamna tsakanin shekarar 2007 da 2015 ya gurfanan a kotu ne akan rashawan N5bn lokacin da yake mulki.

Kwamandan NSCDC, Mr Philip Ayuba, ya bayyana wannan ne ga manema labarai a garin Minna.

Gurfanar da Babangida Aliyu : Hukumar NSCDC ta tura hafsohi 95 domin tabbatar da tsaro a kotu

Gurfanar da Babangida Aliyu : Hukumar NSCDC ta tura hafsohi 95 domin tabbatar da tsaro a kotu

Ayuba yace an basu umurni su tabbatar da tsaro a kotun da za’a gurfanar da tsohon gwamna.

“Zamu ci ma duk wanda yayi kokarin tayar da kuran mazauna wannan wuri.”

KU KARANTA: El-Rufai ya sifanta El-Zakzaky a matsayin dabba

Yayi kiraga jama’an garin su kasance masu biyayya ga doka kuma u cigaba da ayukan gabansu cikin kwanciyan hankali saboda akwai tabbacin tsaro a wurin.

Amma daga baya kuma, wata gamayyar jami’an NSCDC da DSS sunyi zagaye a garin Minna domin tabbatar da cewa basu baya da kura ba.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Tirkashi! Har yanzu akwai al'ummomin da ke riko da al'adan kashe tagwaye a Abuja

Tirkashi! Har yanzu akwai al'ummomin da ke riko da al'adan kashe tagwaye a Abuja

Tirkashi! Har yanzu akwai al'ummomin da ke riko da al'adan kashe tagwaye a Abuja
NAIJ.com
Mailfire view pixel