Canji! Madalla, za'a fara sarrafa wayoyin salula na hannu a Najeriya

Canji! Madalla, za'a fara sarrafa wayoyin salula na hannu a Najeriya

- Wani kamfanin sarrafa wayoyin salula mai suna AfriOne ya bude kamfanin shi na farko a Najeriya

- Kamfanin wanda aka bude a jahar Lagos zai iya sarrafa wayoyi 12,000 a wata

Wayoyin, kirar Android za su sayu akan farashi tsakanin Naira dubu 29 da 33.

Wani babban ma’aikacin kamfanin Lekan Akinjide shi ya bayyana haka a wani taro a jahar Lagos.

NAIJ.com ta tsinkayo shi yana cewa kamfanin ya ci kimanin Dala miliyan 10, kuma kafin karshen shekarar nan, za su bude kamfani a biyu.

A wani labarin kuma, Kasashen Sin Da Ingila sun shiga kawancen huldar kasuwanci na sayan ridi, rogo da waken suya daga hanun kananan manoma na jihar Taraba ta hanyar rabon ingantaccen iri kyauta don baiwa manoman kwarin gwiwa.

Canji! Madalla, za'a fara sarrafa wayoyin salula na hannu a Najeriya

Canji! Madalla, za'a fara sarrafa wayoyin salula na hannu a Najeriya

KU KARANTA: Idan aka raba Najeriya ba arewa kadai zata wahala ba

Gwamnan jihar Taraba Arch, Darius Dickson, ne ya furta haka a lokacin da yake kaddamar da saida takin zamani ton talatin na NPK da Yuriya ga manoma albarkacin daminar bana akan Naira dubu hudu da dari biyar kowani buhu abinda ke nuna rangwamen kashi hamsin idan aka kwatanta da farashinsa a hanun ‘yan kasuwa.

Da yake kaddamar da sayar da takin zamani, ya kuma bada injunan casar shinkafa rance ga manoma da kuma rabon ingantattun irin rogo, ridi da waken soya kyauta.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Wanna jirgin ma dai a Najeriya aka kera shi

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata
NAIJ.com
Mailfire view pixel