Wani babban malami ya yabi shugaba Buhari kan yaki da rashawa

Wani babban malami ya yabi shugaba Buhari kan yaki da rashawa

- Shugaban Limamai na jihar Niger, Sheik Ibrahim Fari, ya yaba ma kokarin shugabna kasa Muhammadu Buhari kan yaki da rashawa a kasar

- Ya ce tuni sashin ya karfafa ma mambobin ta da su rungumi shirin tona-ka-samu na gwamnatin Buhari

Shugaban Limamai na jihar Niger, Sheik Ibrahim Fari, ya yaba ma kokarin shugabna kasa Muhammadu Buhari kan yaki da rashawa a kasar.

Fari ya fada ma kamfanin dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Minna cewa tuni sashin ya karfafa ma mambobin ta da su rungumi shirin tona-ka-samu na gwamnatin Buhari.

Ya bayyana kaddamar da shirin tona-ka-samu a matsayin daya daga cikin abubuwa mafi inganci da ya faru ga kasar a kwanakin nan.

Wani babban malami ya yabi shugaba Buhari kan yaki da rashawa

Babban malami ya yabi shugaba Buhari kan yaki da rashawa

“Zamu ci gaba da wayar da kan mambobin mu muhImmancin yaki da rashawa ta hanyar shirin tona-ka-samu ta gurin tona asirin masu satan kudaden kasa”.

KU KARANTA KUMA: Hukumar sojin sama na Najeriya ta kaddamar da sabon hanyan da zata yaki ta’addanci

Fari ya bayyana cewa kudaden da aka dawo da su ta hanyar tsegumi ya taimaka sosai gurin yaki da rashawa.

Fari ya bayyana cewa rashawa ne dalilin halin da tattalin arziki ke ciki a yanzu.

Fari ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ya kaddamar da tsarin tsaro da zai taimaki yan Najeriya, wadanda ke tona asirin barayin kasa.

Ku biyo mu anan https://www.facebook.com/naijcomhausa/

Da anan https://twitter.com/naijcomhausa

Shin kana iya barin aikin ka don kawo ma gwamnati tsegumi?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel