Yarinya yar shekara 11 ta yi yunkurin kashe mahaifinta a Arewa (Dalili)

Yarinya yar shekara 11 ta yi yunkurin kashe mahaifinta a Arewa (Dalili)

- Labarin ya bulla na yadda wata yarinya mai kimanin shekaru 11 ta yi yunkurin kashe mahaifinta ta hanyar sa masa maganin bera a cikin abinci

- Yarinyar da mahaifinta dake sana'ar kafinta na zaune ne a anguwar Ali Kazaure kusa da babban masallacin Idi na Jos

Majiyar mu ta bayyana cewa mahaifin yarinyar mai suna Muhammad Sani, mutum ne da Allah ya yi wa zafin rai da saurin hannu, wanda ya sa ba ya saurarawa iyalinsa, da zarar wani ya aikata laifi ko kuskure sai ya rika dukan sa, irin dukan fitar hankali, wanda sau da dama har rauni yake yi musu.

NAIJ.com ta tattaro cewa wannan magidanci da shekarun sa ba su wuce 38 zuwa 40 ba, ba ya bambanta dan cikin sa da matarsa wajen azabtarwa. Don haka ne nema cikin shekaru kalilan ya auri mata 6, saboda ba sa yarda su cigaba da zama da shi, bayan jikin su ya gaya musu.

Majiyar mu ta shaida mana cewa, Muhammad Sani na da 'ya'ya 6 wanda kuma akasarin su kowanne uwarsa daban, Khadija na daga cikin yaransa dake zaune ba tare da mahaifiyar su ba a gidan. Kuma ta dade tana kulle da bakin cikin irin wulakanci da cin zarafin da mahaifin ta ya rika yi musu ita da mahaifiyar ta, wanda har ya sa ta tsallake ta bar ta a gidan saboda azaba.

Ran nan matar uban ta yi girki ta ajiye masa abincin sa a gefe kafin ya shiga gida, sai yarinyar ta dauko wani maganin bera da aka ajiye ta barbada a kan abincin ta mayar ta rufe.

Yarinya yar shekara 11 ta yi yunkurin kashe mahaifinta a Arewa (Dalili)

Yarinya yar shekara 11 ta yi yunkurin kashe mahaifinta a Arewa (Dalili)

Da yake ba shi da rabon mutuwa, yana komawa gida ya dauko abinci zai ci sai ya ga wani garin abu da bai gane masa ba, don haka sai ya ajiye bai ci ba. Amma sai ya kira matar ya tambaya ko ta zuba yaji ne a kan abincin ko wani sinadari. Sai dai ta amsa masa ba ita ba ce.

KU KARANTA: Rundunar sojin Sama na Najeriya tayi abun azo a gani

A saboda haka sai aka kira yaran dake gida duk aka bincike su, kowa na cewa ba shi ba ne. Sai ita Khadija ce ta amsa cewa ita ce, amma yayar ta ce ta sa ta. Bayan an tuhumi yayar ita ma ta musanta, daga bisani yarinyar ta amsa laifin ta da kuma dalilin ta.

Khadija ta ce, zuciyar ta kullum na tafasa idan ta ga yadda baban su yake wulakanta iyalinsa ta hanyar cin zarafin su, don haka ta kudiri aniyar kawar da shi daga duniyar ko rayuwar su za ta samu sauki.

Yarinyar dai na cigaba da rayuwa cikin gidan mahaifinta, kawo lokacin rubuta wannan labarin dai babu wani mataki da ya dauka a kan 'yar tasa, bisa yunkurin da ta yi na hallaka shi.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel