Sojoji sun ranta ana kare yayin da yan ƙungiyar asiri suka kashe mutane 20 a Uyo

Sojoji sun ranta ana kare yayin da yan ƙungiyar asiri suka kashe mutane 20 a Uyo

- Wasu matasa yan kungiyar asiri sun bude wuta akan jama'an garin Oku Iboku na jihar Akwa Ibom

- Kimanin mutane 20 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin

Akalla mutane 20 ne suka rigamu gidan gaskiya a garin Oku Iboku na jihar Akwa Ibom yayin da wasu shu’uma matasa suka kai hari.

Shaidun gani da ido sun shaida ma jaridar Daily Post cewar sojojin dake jibge a yankin sun tsere yayin da suka ji harbin mai kan uwa da wabi.

KU KARANTA: An binne gawar Attajiri a kasar Amurka tare da motarsa kamar yadda yayi wasiyya (Hotuna)

Wasu matasa yan kungiyara siri daga garin Ikot Offiong ne suka kai hare haren da muggan bindigu akan wasu jiragen ruwa masu gudu, tare da wurga ma jama’a gurneti.

Sojoji sun ranta ana kare yayin da yan ƙungiyar asiri suka kashe mutane 20 a Uyo

Sojoji

Wani mazaunin garin mai suna Demson Ekong ya shaida ma yan jaridu cewar wasu daga cikin wadanda aka kashe sun hada da mata da kananan yara, tare da gano gawawwakin wasu masulta su tara.

“Jama’an garin Ikot Offiong ne da gwamnatin Kros Ribas suka aiko miyagun mutanen da nufin su karar damu, su karkashe mu kamar kiyashi mazan mu da matanmu. A yanzu haka muna cigaba da gano gawawwaki.” Inji Demson, kamar yadda NAIJ.com ta ruwaito.

Demson ya cigaba da fadin: “Sunyi amfani da bindigu ne daga kan wasu kwale kwale masu gudu, a haka suka dinga harbin mu, hatta sojojin dake gadin iyakan jihohin biyu sai da suka ruga. Sai daga bisani ne suka nemi agaji, inda aka sake aike musu da rundunar sojoji. Da kyar da suka fatattaki matasan.

“Bugu da kari sun tare wasu daga cikin yaran mu, inda suka tafi dasu, tare da kona gidajensu. Amma daga cikinsu sun yi sa’a, yayin da suka fada ruwa, har suka kai wani kauye, a haka suka tsira.” Inji shi

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kaga abinda rikicin kabilanci ke janyowa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel