Tinubu bai taimake ni gurun zama shugaban APC na kasa ba - Oyegun

Tinubu bai taimake ni gurun zama shugaban APC na kasa ba - Oyegun

- John Oyegun ya ce babban jigon jam’iyyar , Bola Tinubu ba shine sanadin zamowar sa shugaban jam’iyyar ta kasa ba

- Oyegun ya bayyana hakan ne a wani hira da jaridar Vanguard

- Shugaban na jam’iyyar APC ya nace kan cewa kowa a jam’iyya ya taimake shi amma babu wani mutun daya wanda ya taimake shi a jam’iyyar

Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress, APC, John Oyegun ya ce babban jigon jam’iyyar , Bola Tinubu ba shine sanadin zamowar sa shugaban jam’iyyar ta kasa ba.

Oyegun ya bayyana hakan ne a wani hira da jaridar Vanguard yayinda yake amsa wani tambayan cewa wasu mutane na zargin cewa baya biyayya ga wadanda suka taimake shi ya zama shugaban jam’iyyar, musamman Bola Tinubu.

Shugaban na jam’iyyar APC ya nace kan cewa kowa a jam’iyya ya taimake shi amma babu wani mutun daya wanda ya taimake shi a jam’iyyar.

Tinubu bai taimake ni gurun zama shugaban APC na kasa ba - Oyegun

Oyegun ya ce Tinubu bai taimake shi gurin zama shugaban APC na kasa ba

A cewar Oyegun, “Kowa ya taimake ni zuwa wannan matsayi sannan kuma ina godiya ga dukkan su. Abu daya shine mutunci da kuma kirkina; bana wasa da wadannan abubuwan guda biyu saboda sune abunda na dogara da su kuma zan tsaya a kansu a ko wani lokaci.

KU KARANTA KUMA: Jami’an tsaro sun dakile harin da yan Boko Haram suka kai a Adamawa

“Ban amince da cewani wani mutun guda ne ya taimaki ne zuwa wannan matsayi ba, kowa ya taimake ni kuma wata rana, za’a bayyana labarin yadda shugaban APC.

"A lokacin zaka ga dukkanin mutanen da suka taimake ni na zamo shugaban jam’iyyar. Wannan na nufin cewa ni na kowa ne. kuma bana daga cikin ko wani sansani a APC. Ni na dukkan yan jam’iyyar APC ne."

Ku biyo mu anan https://www.facebook.com/naijcomhausa/

Da anan https://twitter.com/naijcomhausa

An maka shugaban EFCC na da a Kotu.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel