El-Zakzaky dabba ne – Gwamna Nasir El-Rufai (Bidiyo)

El-Zakzaky dabba ne – Gwamna Nasir El-Rufai (Bidiyo)

-Gwamnan jihar Kaduna tayi wata Magana mai girma

-“Na san El-zakzaky, mun kasance dalibai a jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya”

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya siffanta shugaban kungiyar yan Shi’an Najeriya, Ibrahim El-Zakzaky a matsayin dabba.

El-Rufai wanda yayi wannan furuci a shirin ‘Hard Copy’ na tashar talabijin Channels ya nanata maganarsa duk da cewa wanda suke hiran tare tace masa ya janye maganar, yace baiyi hakan domin cin mutuncin shugaban Shi’an ba.

Ya kara da cewa matsalarsa da kungiyar El-Zakzaky shine rashin amincewa da cewa akwai shugabancin gwamnatin Najeriya.

El-Zakzaky dabba ne – GwamnaNasirEl-Rufai (Bidiyo)

El-Zakzaky dabba ne – GwamnaNasirEl-Rufai (Bidiyo)

Game da cewar El-Rufai, Yan Shi’a yan Najeriya ne kuma suna da hakkin yin addininsu, bamu da matsala da wannan. Wadanda suke zanga-zanga domin sakin El-Zakzaky, ba dukkansu bane yan shi’ a.

“A jihar Kaduna, akwai wasu kungiyoyin Shi’a 2 da basu zanga-zanga, basu tare hanyoyi, kuma sun amince da shugaban kasa da kuma ni a matsayin gwamnan jihar kuma bamu da matsala da su.

KU KARANTA: Rikici ta balle a jihar Legas

“Wadanda muke da matsala da su sune mabiya El-Zakzaky, basu amince da shugaban kasan Najeriya ba, basu amince da ni a mtsayin gwamna ba. Amincewarsu nag a wani kasa ne daban kuma suna kokarin zamar da Najeriya kasar Musulunci.

“Na san El-zakzaky, mun kasance dalibai a jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, mun kasance yan fafutuka a kungiyar dalibai musulumai, saboda haka na san dabban da nike fama da shi. Yawancin masu maganganu akan wannan abu basu san tarihi ba, ina ABU lokacin da aka kori El-Zakzaky, na san shi.”

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel