YANZU YANZU: Sarki Sanusi ya kashe naira biliyan 2.9, ba naira biliyan 6 ba, cikin shekaru uku

YANZU YANZU: Sarki Sanusi ya kashe naira biliyan 2.9, ba naira biliyan 6 ba, cikin shekaru uku

- Masarautar Kano tayi watsi da ikirarin cewa sarki, Muhammadu Sanusi II, ya kashe naira biliyan 6 na asusun masarautar tunda ya hau karagar mulki

- babban jami’in masarautar dake kula da kudade wanda ya kasance Walin Kano, Bashir Wali, ya fada wa masu kawo rahoto cewa masarautar ta kashe naira biliyan 2.9 ne kacal tun da Mallam Sanusi ya hau kujerar sarauta

A ranar Litinin, 24 ga watan Afrilu, masarautar Kano tayi watsi da ikirarin cewa sarki, Muhammadu Sanusi II, ya kashe naira biliyan 6 na asusun masarautar tunda ya hau karagar mulki.

A wani taron manema labarai a Kano, babban jami’in masarautar dake kula da kudade wanda ya kasance Walin Kano, Bashir Wali, ya fada wa masu kawo rahoto cewa masarautar ta kashe naira biliyan 2.9 ne kacal tun da Mallam Sanusi yah au kujerar sarauta a watan Yuli 2014.

KU KARANTA KUMA: Ka ji adadin kudin da Ibrahim Magu ya bankado a wannan shekarar

Mallam Wali, wanda ya samar da wasu bayanai a kan yadda aka kashe kudaden, ya kuma yi bayanin cewa sarki Sanusi ya gaji naira biliyan 1.9 ne ba wai naira biliyan 4 ba kamar yadda ake fada a wasu kafofin watsa labarai ba.

YANZU YANZU: Sarki Sanusi ya kashe naira biliyan 2.9, ba naira biliyan 6 ba, cikin shekaru uku

Sarki Sanusi ya kashe naira biliyan 2.9, ba naira biliyan 6 ba, cikin shekaru uku

Sannan ya ce fadar za ta bayar da hadin kai ga binciken da hukumar yaki da cin hanci ta jihar ta fara.

Muhiyi Magaji ya ce binciken ya zama dole saboda korafe-korafen da jama'a da dama suka gabatar a gaban hukumarsa.

Ku biyo mu anan https://www.facebook.com/naijcomhausa/

Da anan https://twitter.com/naijcomhausa

Har gobe shugaba Buhari na da magoya baya.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel