Takarar shugaban ƙasa a 2019: ‘Ina matukar son ganin Najeriya ta cigaba’ – El-Rufai (Bidiyo)

Takarar shugaban ƙasa a 2019: ‘Ina matukar son ganin Najeriya ta cigaba’ – El-Rufai (Bidiyo)

- Gwamnan jihar Kaduna ya musanta raderadin da ake yi masa na tsayawa takarar shugaban kasa

- Gwamnan yace ba shi da burin takara, amma fa ya damu da Najeriya sosai

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya bayyana cewar bashi da sha’awar takarar shugaban kasa a shekarar 2019.

El-Rufai ya bayyana haka ne yayin wata hira da yayi a gidan talabijin na Channels, inda ya musanta zargin da ake yi masa na cewa wai yana da sha’awar takarar shugaban kasa a 2019.

KU KARANTA: “Dalilin daya sa gwamna Yahaya Bello ke son kashe ni” – Dino Melaye

An tambaye shi: “Shin wannan cece-kuce da ake yawan jinka dasu, anya ba alamun sha’awar takarar shugaban kasa kake da shi ba?”, amma sai El-Rufai yace bashi da wani nufin tsayawa takara, ko kadan.

Takarar shugaban ƙasa a 2019: ‘Ina matukar son ganin Najeriya ta cigaba’ – El-Rufai (Bidiyo)

El-Rufai

“Ina da sha’awar cigaba da karo karatu, saboda ina samun nasarori a karatu”. El-Rufai yaci gaba da fadin.

“An sha zargi na da burin tsayawa takara tun a shekarar 2007, wannan ne ya sa Umaru Yar’adua yasa min ido.

“Haka zalika shima Jonathan ya fara jin haushi na tun bayan da na shiga CPC, muka fara aiki, sai mukarrabansa suka dinga fada mai ai ni ne zanyi takarar shugaban kasa.

“Kun ga, ban taba sha’awar tsayawa takarar shugaban kasa ba, ban ma taba sha’awar tsayawa takarar gwamna ba, har sai da shugaban kasa Muhamamdu Buhari ya nemi in tsaya.” Inji El-Rufai.

“Gaskiya ne na damu da Najeriya don ganin ta cigaba, amma bani da burin tsayawa takara.” Inji El-rufai Kamar yadda NAIJ.com ta ruwaito.

Ga bidiyon nan:

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Rikicin kudancin Kaduna

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel