Maye gurbin sakataran tarayya : Da yiwuwan a baiwa Oshiomole

Maye gurbin sakataran tarayya : Da yiwuwan a baiwa Oshiomole

- Adams Oshiomhole ko sanata Olorunnibe Mammora zasuyi iya maye gurbin sakataren gwamnatin tarayya

- An dakatad da Lawan ne bisa ga zargin rashawa a fadar shugaban kasa

Da yiwuwan a dauko tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomole, ko sanata Olorunnibe Mammora domin maye gurbin kujeran sakataran gwamnatin tarayyan da aka dakatar, Babachir David Lawal.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dakatad da Lawal ne bisa ga zargin almundahana a kudin fadar shugaban kasa na yankin arewa maso gabas.

Kana kuma an dakatad da shugaban hukumanr leken asirin tarayya, Ayo Oke, bisa ga kudin da hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta gani a Ikoyi, jihar Legas.

KU KARANTA: Rikici ta balle a taron jana'izan sanatan da ya rasu

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada wata kwamitin bincike karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, da kuma NSA, Babagana Munguno da ministan shari’a Abubbakar Malami.

Jaridar Thisday ta bada rahoton cewa, an sanar da tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomole da tsohon shugaban maras rinjaye a majalisan dattawa, Mammora a matsayin wadanda kan iya maye gurbin Babachir.

Majiyar tace : "Abinda mutane suka sani shine da wuya Babachir ya tsira daga cikin binciken da ake gudanarwa, saboda haka an samar da wasu sunaye.

“Sunayen da sukafi karfi shine na Adams Oshiomola da Olorunnimbe Mamora.”

https://web.facebook.com/naijcomhausa/?ref=bookmarks

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

NAIJ.com
Mailfire view pixel