An kama wasu ýan kasashen waje su 3 a cikin Boko Haram

An kama wasu ýan kasashen waje su 3 a cikin Boko Haram

- Dakarun soji sun samu nasarar cafke wasu yan kasar waje daga kungiyar Boko Haram

- Rundunar sojin ta bayyana wadanda ta kama a matsayin yan kasar Chadi ne

Rundunar mayakan soja kasa ta smau nasarar cafke wasu matasa su uku yan kasar Chadi daga cikin mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram.

Jaridar TheCables ta ruwaito kaakakin runduna ta 28 dake Mubi Akinloye Badare yana fadin an kama matasan yan kasar Chadi ne biyo bayan wani hari da suka kai a kan iyakar jihohi Borno da Adamawa, sai dai basu smau nasara ba.

KU KARANTA: Jami’an tsaro sun dakile harin da yan Boko Haram suka kai a Adamawa

Akinloye ya bayyana cewa dakarun soji sun dakile harin da yan ta’addan suka yi nufin kawo wa garin Madagali na jihar Adawama da kuma Liman Kara na jihar Borno.

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito Akinloye yana sanar da kamen kamar haka: “Mayakan da muka kama su uku yan kasar Chadi ne.”

An kama wasu ýan kasashen waje su 3 a cikin Boko Haram

Sojoji a bakin aiki

Akinloye yace sun yi musayar wuta sosai da yan ta’addan har na tsawon awanni uku kafin daga bisani suka ci galaba akan su.

Bugu da kari, inji Kaakakin, “kafin wannan yunkurin harin ta’addancin, bataliya ta 192 ta kashe yan Boko Haram guda shidda a kauyen Dissa da Patawa na jihar Borno."

Dama dai ko a baya an sha faman artabu tsakanin jami’an soji da yan Boko Haram a garin Limankara dake kan iyakar kasar Kamaru da jihar Borno.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli jimamin da Boko Haram ta sa jama'a

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

NAIJ.com
Mailfire view pixel