Yadda wani Sanata ya rasu ana zaune kalau

Yadda wani Sanata ya rasu ana zaune kalau

– Sanata Isiyaka Adeleke ya bar Duniya jiya

– Adeleke ya taba yin Gwamna shekarun baya

– Kwatsam kawai sai aka ji labari cewa Sanatan ya cika

A jiya kwatsam sai aka ji labari cewa Sanata Isiyaka Adeleke ya bar Duniya. A shekaran jiya dai yana nan kalau tare da Jama’ar sa a gida. Mutanen Osun dai sun yi bakin cikin rasuwar tsohon Gwamna da kuma Sanatan na su.

Yadda wani Sanata ya rasu ana zaune kalau

Majalisa tayi jimamin rashin Sanata

Sanata Adeleke shi ya fara rike Gwamnan Jihar Osun bayan an ba ta Jiha tun yana dan shekaru 30 da ‘yan-kai. A wancan lokaci yayi gwagwarmaya bayan da Soji suka soke zaben MKO Abiola a shekarar ‘93.

KU KARANTA: Arewa ba Matsiyata bane Inji Falalu Bello

Yadda wani Sanata ya rasu ana zaune kalau

Sanata Adeleke ya rasu yana shekaru 62

Har yanzu haka dai Adeleke ya bar Duniya ne da barin zama Gwamna inda har ya fara shirin yawon kamfe. Adeleke na sa ran fitowa takarar Gwamna da zarar wa’adin Gwamna Rauf Aregbosola ya kare.

Shugaba Buhari ya aika ta’aziyar sa inda ya yaba masa wajen yaki da sata a kasar. Haka-zalika Majalisa tayi ta jimamin rashin sa. Wasu dai na ganin ba mamaki guba aka sa masa a abinci don har an maida gawar sa asibiti. Marigayin dai kawun Mawakin nan ne Davido.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ziyara zuwa kasuwannin Jihar Ogun

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel