Za'a dakatar da jami'an gwamnati da aka zarga da almundahana

Za'a dakatar da jami'an gwamnati da aka zarga da almundahana

- Shugaban Buhari ya bai wa kwamitin da ke bincikar zargin almundahana umarnin dakatar da dukkanin jami’an gwamnatin da ke da alaka da rashawa

- Shugaba kasar dai ya bukaci kwamitin ya dakatar da wadanda ake zargin ne kafin kammala aikinsa na makwanni biyu

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bai wa kwamitin da ke bincika zargin aikata almundahana da ake wa sakataren gwamnati da aka dakatar, Babachir Lawal da babban daraktan hukumar NIA Ayo Oke, umarnin dakatar da dukkanin jami’an gwamnatin da ke da alaka da laifukan da manyan jami'an biyu suka tafka.

NAIJ.com ta samu labarin cewa shugaba Buhari dai ya bukaci kwamitin ya dakatar da wadanda ake zargin ne kafin kammala aikinsa na makwanni biyu.

KU KARANTA KUMA: Jami’an tsaro sun dakile harin da yan Boko Haram suka kai a Adamawa

Kwamitin mai kunshe da mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo a matsayin shugaba, ministan shara’a Abubakar Malami, da kuma mai bai wa shugaban kasa shawara kan tsaro Babagana Mungonu, yana bincike ne kan zargin da ake wa sakataren gwamnati Babachir Lawal bisa bawa kamfanin kwangilar sama da naira miliyan 200 don share ciyawa a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Za'a dakatar da jami'an gwamnati da aka zarga da almundahana

Shugaba Buhari ya dakatar da jami'an gwamnati da aka zarga da almundahana

Zalika kwamitin wanda ya fara aikinsa a ranar Larabar da ta gabata, yana gudanar da bincike kan, dala miliyan 43 da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC ta gano a wani gida, da ke unguwar Ikoyi a jihar Legas, wanda kuma ake zargin darakatan hukumar tattara bayanan sirri ta kasar NIA Ayo Oke da masaniya kan kudin, bayanda yayi ikirarin cewa kudaden mallakar hukumarsa ce.

Ku biyo mu anan https://www.facebook.com/naijcomhausa/

Da anan https://twitter.com/naijcomhausa

Shin kana iya barin aikin ka don kawo ma gwamnati tsegumi?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

NAIJ.com
Mailfire view pixel