An bankaɗo wasu tarin bama bamai da Boko Haram ta binne a Borno

An bankaɗo wasu tarin bama bamai da Boko Haram ta binne a Borno

-Dakarun soji sun gano wasu muggan bama bamai da Boko Haram ta binne akan hanya

-Kwararrun sojoji da suka iya sarrafa Bama bamai sun kwance su

Ayarin wani babban hafsan soa Manjo janar I.M Alkali yaci karo da wasu binnannun bama bamai akan hanyarsu ta zuwa Bama daga garin Gwoza a ranar Asabar 22 ga watan Afrilu.

Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da hafsan sojin ke kan hanyar zuwa rangadi da mislain karfe 9 na safe, inda ya tarar da bama baman da kungiyar Boko Haram ta binne har guda hudu.

KU KARANTA: Operation Harbin Kunama II : Rundunar soji ta gano tafkin makamai a kudancin Kaduna

An iske wadannan bamabamai ne a daidai mahadar hanyar Banjo da Pulka, kimanin kilomita shidda kenan daga garin Firgi, kamar yadda Kaakakin rundunar Birgediya SK Usman ya bayyana.

An bankaɗo wasu tarin bama bamai da Boko Haram ta binne a Borno

Guda cikin bamabaman

NAIJ.com ta ruwaito jami’an rundunar ba suyi wata wata ba, inda aka aika da kwararrun jami’an soja masana sirrin sarrafa bamabamai suka hako su, tare da tayar dasu, ba tare da sun jikkata kowa ba.

Ga sauran hotunan nan:

An bankaɗo wasu tarin bama bamai da Boko Haram ta binne a Borno

Wani cikin bamabaman

An bankaɗo wasu tarin bama bamai da Boko Haram ta binne a Borno

Kwararru suna kwance bama baman

An bankaɗo wasu tarin bama bamai da Boko Haram ta binne a Borno

Yayin da ake kwance bama baman

An bankaɗo wasu tarin bama bamai da Boko Haram ta binne a Borno

Bayan an tayar da bamabaman

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yadda sojoji ke yi ma Boko Haram ruwan wuta

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati

Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati

Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati
NAIJ.com
Mailfire view pixel