YANZU YANZU: Mutane uku sun mutu yayinda yan kunar bakin wake suka kai hari Borno

YANZU YANZU: Mutane uku sun mutu yayinda yan kunar bakin wake suka kai hari Borno

- Yan kunar bakin wake mata uku sun kai harin bam a Maiduguri, babban birnin jihar Borno

- Jami’an tsaro sun harbe biyu daga cikin su har lahira yayinda sukayi yunkurin shiga birnin

- Ta ukun tayi nasarar tayar da kanta kafin bindigogin jami’an tsaro ya kai ga samun ta

- Wadanda suka kai harin ne kawai suka mutu a harin

Jaridar Daily Sun ta ruwaito cewa a kalla mutane uku ne suka mutu bayan yan kunar bakin wake na kungiyar Boko Haram sunyi yunkurin shiga Maiduguri, jihar Borno, a ranar Litinin, 24 ga watan Afrilu.

A cewar rahoton, yan ta’addan ne suka mutu bayan jami’an tsaro na jihar sun dakile harin.

An harbe biyu daga cikin yan kunar bakin waken mata sunyi yunkurin shiga birnin ta kauyen Mamanti a karamar hukumar Jere wanda ke a wajen birnin Maiduguri da kimanin karfe 5:10 na safiyar ranar Litinin.

KU KARANTA KUMA: ALBISHIRINKU: Janaral sojin kasa guda 2 sun tsere daga harin Boko Haram

Daga baya an dakile kayan fashewar dake jikin su.

Kwamishinan yan sandan jihar Borno Damian Chukwu ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa daya daga cikin yan kunar bakin waken uku ta tayar da kanta.

Ku biyo mu anan https://www.facebook.com/naijcomhausa/

Da anan https://twitter.com/naijcomhausa

Kalli wannan bidiyo da NAIJ.com ta kawo maku na Boko Haram dake nuna yarinyar da ta tsira daga harin yan ta’addan Boko Haram a sansanin yan gudun hijira kusa da Abuja

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Tirkashi! Har yanzu akwai al'ummomin da ke riko da al'adan kashe tagwaye a Abuja

Tirkashi! Har yanzu akwai al'ummomin da ke riko da al'adan kashe tagwaye a Abuja

Tirkashi! Har yanzu akwai al'ummomin da ke riko da al'adan kashe tagwaye a Abuja
NAIJ.com
Mailfire view pixel