Ko kun san wacece ta gaji Babachir Lawal? Ga muhimman bayanai 3 game da ita

Ko kun san wacece ta gaji Babachir Lawal? Ga muhimman bayanai 3 game da ita

- Mai rikon mukamin sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya, Dr. Habiba Lawal, ‘yar asalin karamar hukumar Toro ne dake jihar Bauchi

- An haifeta a ranar 3, ga watan yuni shekarar 1963, tayi karatun firamare a makarantar firamare na Gyamzo a garin Toro, daga nan sai karatun sakandare wanda tayi a kwalejin gwamnatin tarayya dake Kaduna

NAIJ.com ta bi diddiki domin ganin kawo maku wasu muhimman al'amurra uku da ya kamata ku sani game da ita din. Kuma gasu kamar haka:

1. Bayan da ta kammala karatun sakadare sai ta nufi jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria, a inda tayi digiri dinta na farko da na biyu, daga bisani kuma ta tafi jami’ar Abubakar Tafawa Balewa inda tayi digirin digirgir.

Har ila yau tayi wani karatun a wata jami’a mai suna Anglia a kasar Biritaniya.

Ko kun san wacece ta gaji Babachir Lawal? Ga muhimman bayanai 3 game da ita

Ko kun san wacece ta gaji Babachir Lawal? Ga muhimman bayanai 3 game da ita

KU KARANTA: Rikici ya barke a wajen ta'aziyyar Sanata

2. Dr Habiba Lawal, ta yi koyarwa a jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, dake Bauchi, tayi kwamishina, a ma’aikatun ciniki da masana’antu da ma’aikatar al’adu da yawon bude ido a jihar Bauchi, ta kuma rike mukamai daban daban a matakin gwamnatin tarayya.

3. Dr Habiba Lawal, ita ke rike da mukamin babbar jami’a a ofishin sakataren gwamnatin tarayya kawo lokacin da aka tabbatar mata da mukamin sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya amma a matsayi na riko.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Ku kalli jawabin wani dan APC

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel