EFCC: Sabon tsarin gano kudin sata na aiki ainun

EFCC: Sabon tsarin gano kudin sata na aiki ainun

– Shugaban EFCC Magu ya bayyana irin nasarar da Hukumar sa ta samu

– Magu yace EFCC ta bankado makudan kudi ta sanadiyar sabon tsarin wannan Gwamnati

– Ibrahim Magu yace babu gudu babu ja da baya wajen yaki da sata a kasar nan

EFCC: Sabon tsarin gano kudin sata na aiki ainun

Shugaban Hukumar EFCC Magu

Dazu NAIJ.com ta kawo labarin irin makudan kudin da Hukumar EFCC ta bankado wanda ya kai Naira Biliyan 17 cikin watanni 4 rak. Ibrahim Magu ya kara shan alwashin cewa sai ya ga bayan satar dukiyar Jama’a a Najeriya.

Kuna da labari sabon tsarin nan da aka kawo na tona-ka-samu-rabon da Gwamnatin Buhari ta kawo ya taimaka matuka wajen gano kudin da aka sace a kasar nan. A dalilin hakan an samu N521, 815, 000.000 da kuma Dalar Amurka $53,272,747.000, da Fam na Ingila £122.890.00 da Dalar Euro €547,730.00.

KU KARANTA: An fara binciken masarautar Kano

EFCC: Sabon tsarin gano kudin sata na aiki ainun

EFCC na ta gano kudin sata

A sabon tsarin da aka kawo wanda ke bada damar wanda ke da wani asiri na wasu kudi da aka sace ya sanar da Hukumar EFCC. Daga nan idan an samu nasara za a mika masa rabon sa cikin kwanciyar hankali.

A Ranar Juma’a mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya gana da shugaban na EFCC Ibrahim Magu har na tsawon lokaci inda aka nemi bayani game da irin kudin da Hukumar sa ta karbe daga hannun barayi.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Sabon tsarin Gwamnati na gano kudin sata a Najeriya

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ko kun san adadin Yara da aka ketawa haddi a Sansanan Gudun Hijira cikin watannin hudu

Ko kun san adadin Yara da aka ketawa haddi a Sansanan Gudun Hijira cikin watannin hudu

Ko kun san adadin Yara da aka ketawa haddi a Sansanan Gudun Hijira cikin watannin hudu
NAIJ.com
Mailfire view pixel