‘Yan kudu sun mana nisa; amma mu Arewa ba matsiyata ba ne

‘Yan kudu sun mana nisa; amma mu Arewa ba matsiyata ba ne

– Dan Masanin Zazzau Alhaji Falalu Bello yace an yi mana nisa a Arewa

– Sai dai fa duk da haka yace bai yiwuwa ace Arewa ta fi kowa talauci

– Falalu Bello yace idan aka raba kasar nan kowa zai sha wahala

‘Yan kudu sun mana nisa; amma mu Arewa ba matsiyata ba ne

Sarkin Kano tare da Ooni na Ife

Kwararren Ma’aikacin bankin nan Alhaji Falalu Bello ya bayyana cewa Kudancin kasar nan sun yi wa Arewa nisa duk da cewa da ana tafiya kafada-kafada. Yanzu an yi Arewacin kasar wani finitinkau.

Tsohon shugaban Bankin nan na Unity ya bayyana cewa ko da an bar Arewa a baya ba daidai bane ace kuma ita tafi kowane Yanki talauci a Najeriya kamar yadda Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya bayyana. Bello yace Inyamurai suna nan sun cika Arewa suna neman na abinci.

KU KARANTA: Farashin shinkafa ya sauko a Kaduna

‘Yan kudu sun mana nisa; amma mu Arewa ba matsiyata ba ne

Arewa ba matsiyata ba ne Inji Falalu Bello

Danmasanin Zazzau din ya bayyana wannan ne a wata hira da yayi da Jaridar Daily Trust kamar yadda muka samu labari. Alhaji Falalu Bello yace Arewacin kasar nan na da arzikin kasa na noma. Yake cewa tun daga lokacin tsohon shugaban kasa Ibrahim Babangida aka kashe harkar noma a Najeriya.

Kwanan NAIJ.com ta fara samun jita-jitar cewa wasu Gwamnonin Arewa na kokarin tsige Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II. Yanzu an tabbatar da cewa an fara binciken fadar saboda korafi da Jama’a su ka rika kai wa na barna da kudi.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wani Fasto ya karbi Musulunci

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Tirkashi! Har yanzu akwai al'ummomin da ke riko da al'adan kashe tagwaye a Abuja

Tirkashi! Har yanzu akwai al'ummomin da ke riko da al'adan kashe tagwaye a Abuja

Tirkashi! Har yanzu akwai al'ummomin da ke riko da al'adan kashe tagwaye a Abuja
NAIJ.com
Mailfire view pixel