“Dalilin daya sa gwamna Yahaya Bello ke son kashe ni” – Dino Melaye

“Dalilin daya sa gwamna Yahaya Bello ke son kashe ni” – Dino Melaye

- Sanata Dino Melaye ya zargi gwamnan Kogi Yahaya Bello da shirin kashe shi

- Melaye yace kokarinsa na kwatar ma talakawa yancinsu ne ya sa haka

Sanatan al’ummar Kogi ta kudu, Dino Melaye ya bayyana dalilin daya gwamnan jihar Kogi ke kokarin halla kashi, inda yace ba komai ya sa haka ba illa kokarin kwatar ma yan fansho hakkokinsu dayake yi.

Melaye ya bayyana haka ne a lokacin dayake ganawa da kungiyar matan mazabarsa, bayan sun gudanar da zanga zangar nuna bacin ransu da harin da aka kai ma Sanatan a ranar Asabar 22 ga watan Afrilu.

KU KARANTA: Tattalin arziki: Naira na cigaba da rike wuta

Melaye yace ma’aikata da yan fansho a jihar Kogi na cikin bakar wahala, biyo bayan rashin biyansu albashinsu na watanni 15 da kuma kudin fansho da gwamnatin ta gagara biyan yan fanshon ta.

“Dalilin daya sa gwamna Yahaya Bello ke son kashe ni” – Dino Melaye

Dino Melaye

NAIJ.com ta jiyo Melaye yana cewa: “Gwamnatin tarayya ta baiwa Yahaya Bello naira biliyan 20 a matsayin tallafi, ama yaki ya biya ma’aikata hakkinsu, sa’annan an bashi naira biliyan 11, duk da haka yaki biyan ma’aikata.”

Melaye bai tsaya nan ba, “a halin da ake ciki, yara sun daina zuwa makaranta, yan haya sun kasa biyan kudin haya, don haka ba zmau yarda ba, mutanen Kogi sun gaji da wannan gwamnatin.”

Ba komai bane ya kawo wannan wahalar illa gwamnatin Yahaya Bello da shugaban karamar hukumar mu ISsa Taofiq.

Idan ba’a manta ba dai a satin daya gabata ne Melaye yace wasu yan bindiga sun kai mai hari a gidansa dake jihar Kogi, sai dai basu same shi a gidan ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Jigo a APC ya bayyana dalilin da zai sa jam'iyyar ta fadi zabe

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel