“Zamu shigo da sabbin jiragen kasa guda 20 a watan Yulio” – Amaechi

“Zamu shigo da sabbin jiragen kasa guda 20 a watan Yulio” – Amaechi

- Gwamnatin Buhari zata kara yawan jiragen kasa da ake amfani dasu a kasar nan

- Ministan sufuri, Rotimi Amaechi yace zasu karo jiragen kasa guda 20

Ana sa rana harkar sufurin jiragin kasa zai kara habbaka zuwa karshen watan Yulio na bana, kamar yadda ministan sufuri Rotimi Amaechi ya sanar, inda yace za’a shigo da sabbin jiragen kasa guda 20.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Amaechi yana fadin haka ne yayin wata ganawa da yayi da manyan masu tace labaru, inda yace:

KU KARANTA: Tattalin arziki: Naira na cigaba da rike wuta

“Zuwa taskiyar watan Yulio zamu samu karin jiragen kasa guda 20, burinmu shine zuwa karshen shekarar na mu samu jiragen kasa da yawa, a ko ina a fadin kasar nan, kamar yadda muke dasu a baya.”

“Zamu shigo da sabbin jiragen kasa guda 20 a watan Yulio” – Amaechi

Minista Amaechi

Amaechi ya tabbatar ma yan Najeriya cewa zuwa 29 ga watan Mayu, ranar da gwamnatin Buhari ke cika shekaru 2 akan mulki, zasu gamsu da kokarin da shugaba Buhari ke yin a ganin an samar da wadatattun hanyoyin jiragen kasa a fadi kasar nan.

Amaechi yace manufar shirin iganta hanyoyin jiragen kasa shine don samar da hanyar fitar da kayayyakin amfanin gona a saukake zuwa birane da manyan garuruwa, wanda hakan zai sanya kayan masarufin yin arha.

“Zamu shigo da sabbin jiragen kasa guda 20 a watan Yulio” – Amaechi

Sabon jirgin kasa a Najeriya

Majiyar NAIJ.com ta jiyo Amaechi yana fadin: “Muddin muka cimma burinmu na samar da isassun jiragen kasa a Najeriya, tabbas farashin kayan abinci zai karye, kamar yadda muka yi akan farashin tumatir watannin da suka gabata.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli yadda jirgin kasa ke tafiya a Najeriya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel