Bango ya tsage a ƙungiyar Boko Haram: Ɓangarori na yaƙar juna

Bango ya tsage a ƙungiyar Boko Haram: Ɓangarori na yaƙar juna

- An samu rarrabuwan kai tsakanin yayan kungiyar Boko Haram

- Kwamandan yaki na rundunar sojojin kasashen tafkin Chadi yace alamun nasara ne

Kwamandan rundunar hadaka ta yankin tafkin Chadi Manjo janar Lmidi Adeosun yace rundunar soji na amfani da barakan dake tsakanin yayan kungiyar Boko Haram wajen murkushe kungiyar ta’addancin.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito bangarorin da suka bayyana sun fito ne a tsagin Abubakar Shekau da muma tsagin Al-Barnawi.

KU KARANTA: Jami’an tsaro sun dakile harin da yan Boko Haram suka kai a Adamawa

Kwamandan rundunar ya bayyana haka ne yayin dayake amsa tambayoyin yan jaridu kan yadda samuwar bangaren Al-Barnawi ke shafan kokarinsu na murkushe kungiyar.

Bango ya tsage a ƙungiyar Boko Haram: Ɓangarori na yaƙar juna

Manjo janar Lamidi

Kwamanda Adeosun na daga cikin hafsan sojin kasashen Afirka da suka yi wata tattaunawa ta wayar tarho wanda gwamnatin kasar Amurka ta shirya musu don basu horo da kuma gogar dasu. Cikin wadanda suka zamu shiga hirar, har da kwamandan rundunar sojojin Amurka dake Afirka.

Kwamanda Amosun yace barazanar da Al-Barnawi yayi na cewa zai kai ma sojoji hari, da gaske yake, saboda mun fahimci ya fara kokarin aiwatar da manufarsa, amma suma sojoji basu yi kasa a gwiwa ba.

“Yana yawan kai ma Sojoji hare hare, kuma muna sane da lokacin daya balle daga bangaren Shekau, kuma har ya samu wasu daga ISIS suna goya masa baya.” Inji shi.

Sai dai Kwamandan yace “Muna amfani da wannan daman barakan dake tsakaninsu, musamman yadda suka sanya Shekau cikin tsaka mai wuya.” Kamar yadda NAIJ.com ta ruwaito.

Bango ya tsage a ƙungiyar Boko Haram: Ɓangarori na yaƙar juna

Shekau da Albarnawi

Kwamandan rundunar sojin Amurka dake nahiyar Afirka yace manufar kasar Amurka na shiga cikin wannan rikici shine don magance ta’addanci a nahiyar, don haka ne ma suka shirya wannan taron kara ma juna sani tare da horar da kwamandojin yaki a Afirka.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Iyayen yan matan da Boko Haram ta sace sun yi magiya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

NAIJ.com
Mailfire view pixel