Hukumar sojin sama na Najeriya ta kaddamar da sabon hanyan da zata yaki ta’addanci

Hukumar sojin sama na Najeriya ta kaddamar da sabon hanyan da zata yaki ta’addanci

- Hukumar sojin sama ta kaddamar da sabon hanyan da zata yaki ta’addanci

- Ta samar da jirgin sama mai saukan ungulu na MI-35M

Ranar hukumar sojin sama (NAF) na shekarar 2017 ya zo karshe a Makurdi, jihar Benue tare da kaddamar da sabbain jiragen sama masu saukan ungulu na MI-35M guda biyu.

An kuma gabatar da Karin matsayi ga sabon shugaban ayyuka na musamman (SOC) da kuma lambar yabo na tukin jirgi ga matukan hukumar soji guda 6. Sabbabin matukan jirgin sun hada da mutane 2 daga makarantar King Hussain Air College Jordan da kuma mutane 4 daga International Helicopter Flying School, Enugu.

Kaddamar da sabon jiragen mai dauke da bindigogi zai taimaki ayyukan hukumar sojin sosai da kuma basu karfin yaki da ta’addanci da ko wani irin laifuka a kasar. Sabon jirgin hari na Mi-35M na da karfin aiki da dare kuma ya fi wanda suke da shi a bayahar ila yau yafi inganci gurin aiki,kuma sannan yana da gilashin hangen nesa wanda zai bari a hankalta a lokacin aiki.

Hukumar sojin sama na Najeriya ta kaddamar da sabon hanyan da zata yaki ta’addanci

Hukumar sojin sama na Najeriya ta kaddamar da sabbabin jiragen sama masu saukar ungulu

Shugaba kuma babban kwamandan hukumomin tsaro, Muhammadu Buhari wanda ministan tsaro Mansur Mohammad Dan-Ali ya wakilce shi ne ya kaddamar da taron. Da yake magana a lokacin taron, shugaban ya bayyana cewa kaddamar da jiragen a hukumar sojin zai kara masu inganci a kan aikin su.

KU KARANTA KUMA: ALBISHIRINKU: Janaral sojin kasa guda 2 sun tsere daga harin Boko Haram

A cewar shugaban, nasarar da hukumar sojin ta yi a kan yan ta’addan Boko Haram ya tabbata ne ta hanyan horo da kayayyakin ayyukan da hukumar da sauran hukumomin tsaro ke samu.

NAIJ.com ta tattaro maku sauran hotuna daga taron.

Hukumar sojin sama na Najeriya ta kaddamar da sabon hanyan da zata yaki ta’addanci

Jami'an hukumar sojin sama a lokacin taron

Hukumar sojin sama na Najeriya ta kaddamar da sabon hanyan da zata yaki ta’addanci

Hukumar sojin sama na Najeriya ta kaddamar da sabon hanyan da zata yaki ta’addanci

Hukumar sojin sama na Najeriya ta kaddamar da sabon hanyan da zata yaki ta’addanci

Hukumar sojin sama na Najeriya na shirin kawo karshen yan ta'addan Boko Haram

Ku biyo mu anan https://www.facebook.com/naijcomhausa/ Da anan https://twitter.com/naijcomhausa

Shin kana iya barin aikin ka don kawo ma gwamnati tsegumi?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel